Idan Buhari Ya Ba Mutum Mukami, Sai Ayi Shekaru 4 Bai Waiwaye Shi – Tsohon Minista
- Tsohon Ministan ma’aikatar sadarwa ya yi karin haske a kan yadda Muhammadu Buhari ya sha bam-bam da Bola Ahmed Tinubu
- Adebayo Shittu ya ce a lokacin da su ke ofis tsakanin 2015 da 2019, Shugaban kasa bai cika bibiyar halin da Ministocinsa ke ciki ba
- Cif Shittu yake cewa salon da Shugaba Tinubu ya dauka dabam kuma zai yi kyau a rika waiwayen duk wadanda aka ba mukamai
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Adebayo Shittu wanda ya yi Ministan ma’aikatar sadarwa a gwamnatin tarayya, ya yi magana kan salon mulkin Muhammadu Buhari.
Da ake hira da shi a tashar Channels a ranar Alhamis, Cif Adebayo Shittu ya tofa albarkacin bakinsa game da horar da mukarrabai da ake yi.
Gwamnatin tarayya ta shirya bita na musamman domin Ministoci, Hadimai, Mukarrabai da sauran Jami’an gwamnati su samu kwarewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Buhari da Gwamnatin Tinubu
Adebayo Shittu ya ce a lokacinsu, Mai girma Muhammadu Buhari bai bi sahun da Mai girma Bola Tinubu yake dauka bayan hawa mulki ba.
Daily Trust ta rahoto Shittu ya na cewa a baya, ba a kula sosai da abubuwan da wadanda ake ba mukami su ke yi, akasin salon Bola Tinubu.
"Buhari bai yi wa kowa barazana ba. Kamar yadda na fada, Buhari ba Tinubu ba ne kuma Tinubu ba Buhari ba ne.
Abin da na sani game da Buhari duk da girmama shi da na ke yi, mutum ne shim ai zurfin ciki wanda bai da hayaniya.
Idan ya ba mutum aiki, ba zai taba tambayar yadda aka yi da shi ba.
Dole in fadi wannan saboda kishin kasa domin gwamnatin da za ta zo bayan shi ta dauki mataki a kai.
A gwamnatin Buhari, idan ba ka je ka neme shi ba, watakila sai ayi shekaru hudu bai waiwaye ka."
- Adebayo Shittu
Buhari bai yi wa Ministoci bita ba?
Sai dai Legit ta bincika kuma ta gano daga baya gwamnatin Buhari ta shirya irin wannan taron bita har sau uku kafin ya bar mulki a Mayun nan.
Taron karshe da aka yi a Oktoban 2022 ne, kafin nan an yi makamancinsa a 2021 saboda a rika bibiyar kokarin da ma’aikatu su ke yi a Najeriya.
PDP da APC duk uwarsu daya - Shittu
Da ya zanta da 'yan jarida a 2023, an ji labari Adebayo Shittu ya ce Jam'iyyar APC ba ta da wata marabar akida da manufofi da PDP da aka kifar.
Shittu ya ji tsoron cewa jam'iyyarsu ta APC mai mulki za ta ya shan kashi a zabe.
Asali: Legit.ng