Majalisar Tarayya Ta Amince da Ƙarin Kasafin Kuɗin 2023 Wanda Tinubu Ya Aiko Mata, Bayanai Sun Fito

Majalisar Tarayya Ta Amince da Ƙarin Kasafin Kuɗin 2023 Wanda Tinubu Ya Aiko Mata, Bayanai Sun Fito

  • Majalisun tarayya sun amince da buƙatar shugaba Bola Tinubu na kara N2.17tr a kasafin kuɗin 2023 karo na biyu kenan
  • Wannan mataki ya biyu bayan tsallake karatu na uku da kasafin ya yi da kuma aminta da rahoton zaman haɗin guiwa na majalisun biyu
  • Shugaba Tinubu ya kara zunzurutun kuɗin ne domin cike gurbin ƙarin albashi, tallafin kudi ga talakawa da tsaron kasa

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja -Majalisar dattawan da majalisar wakilan Najeriya sun amince da kunshin ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2023 wanda ya kai N2.17tr bayan tsallake karatu na uku.

Hakan na nufin sabon ƙarin kasafin kuɗin ya zama doka kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rusau: Kotu Ta Umarci Gwamnatin Abba Ta Biya ‘Yan Kasuwa N30bn Nan da Kwanaki 7

Majalisar tarayya NASS.
Majalisar Tarayya Ta Amince da Ƙarin Kasafin Kuɗin 2023 Wanda Tinubu Ya Aiko Mata, Bayanai Sun Fito Hoto: NASS
Asali: Facebook

Gabanin amincewa da kudirin ƙarin kasafin, majalisar dattawa ta karɓi rahoton zaman haɗin guiwa da aka yi tsakaninta da majalisar wakilan tarayya kan karin kasafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, Sanata Solomon Olamilekan Adeola (APC, Ogun ta yamma) ne ya gabatar da rahoton zaman.

Kudirin ƙarin kasafin ya tsallake karatu na ɗaya, na biyu da na uku a dukkan majalisun tarayyan guda biyu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar mambobin majalisun, wannan ƙunshin kudirin zai amfani ƙasar nan da mutanen cikinta.

Abin da kasafin ya ƙunsa

Shugaba Bola Tinubu, a wata wasika da ya tura majalisun biyu, ya bukaci ‘yan majalisar tarayya da su amince da kudirin, wanda shi ne karo na biyu a cikin wannan shekarar.

Wannan kudirin ƙarin kasafin shi ne karo na biyu a 2023 bayan na farko wanda majalisun biyu suka amince a ƙara N819.5bn domin tallafa wa talakawa su rage radaɗi.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta ba AGF wa'adin sa'o'i 72 domin bayar da ba'asi kan N100bn na tallafin COVID-19

A wasikar, Tinubu ya ce ya zama wajibi a kara matakan jin kai, da suka hada da ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati da kuma tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi.

Majalisar dattawa ta amince Tinubu ya ciyo bashi

A wani rahoton mun kawo muku cewa an amince da bukatar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Tinubu na ciyo bashi.

A zamanta na ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, majalisar dattawa ta amince da bukatar Tinubu na ciyo bashin dala biliyan 7.8 da Yuro miliyan 100.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262