Zakir Naik Ya Sha Suka Saboda Kiran Sojojin Saman Nigeria ‘Sojojin Musulunci’

Zakir Naik Ya Sha Suka Saboda Kiran Sojojin Saman Nigeria ‘Sojojin Musulunci’

  • Malamin addinin Musulunci Zakir Naik ya sha suka a wajen wasu 'yan Nigeria saboda kiran sojojin saman Nigeria 'Sojojin Mulunci'
  • Zakir Naik ya ziyarci Nigeria ne domin gudanar da wasu karatuttuka da wa'azi a garuruwa daban daban na kasar
  • Naik ya wallafa hotunan da ya dauka tare da wasu jami'an sojin saman Nigeria a shafinsa na X, lamarin da bai yi wa wasu dadi ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Dr Zakir Naik, wani babban malamin addinin Musulunci a kasar India, na ci gaba da shan suka bayan da ya alakanta sojojin saman Nigeria da zama 'sojojin Musulunci,' a cewar The Cable

Naik ya kawo ziyara Nigeria ne bisa gayyata daga Sa'ad Abubakar, Sarkin Musulmi, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

“Ni ba waliyyi bane, Najeriya ba ta da matsala”, In ji Peter Obi

Dr Zakir Naik
Ma'abota shafin X suna ci gaba da sukar Dr Zakir Naik kan wasu kalamai da yayi a Nigeria Hoto: Dr Zakir Naik
Asali: Twitter

Malamin addinin Musuluncin, wanda ya iso Nigeria a ranar Litinin, ya wallafa wasu hotuna da ya dauka tare da wasu jami'an sojin saman Nigeria da na imagireshan, inda ya bayyana su da zama sojojin Musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ganawa tare da Musulmin jami'in sojin sama, kaftin Abbas Hashim, kwamandan tashar jirgin sama na hukumar soji da ke Abuja, Nigeria," Naik ya makala rubutun a jikin wani hoto.

An yi wa Zakir Naik Martani

Sai dai wasu daga cikin 'yan Nigeria sun nuna rashin jin dadin yadda Zakir Naik ya alakanta sojojin da zama na Musulunci kawai, musamman a cikin kasa irin Nigeria da ke fama da matsaloli na bambancin addini.

Ga abinda wani yake cewa:

Me ka sha? Ko za ka iya yi mana bayanin abinda kake nufi da sojin sama Musulmai?

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

Shi kuwa @_Victorsmog, cewa yayi:

Wannan lamari ne mai hadari. Yanzu muna da hukumar sojin sama ta Musulmai?

Wani ma ya yi tsokaci:

Su jami'an sojin saman Nigeria ne. Mu Musulman Nigeria ba mu togace kan wata hukuma ta mu bace mu kadai. Don Allah ka girmama ra'ayinmu idan kana cikin kasarmu.

- @OMO_9JA_

Dalilin zuwan Dr Zakir Naik Nigeria

Shahararren malamin addinin Musulunci Dr Zakir Naik ya ziyarci jihar Sokoto, Nigeria, domin halartar bukin mako na Usman Danfodiya karo na 10, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ana gudanar da bukin makon ne a kowacce shekara, bisa jagorancin Sarkin Musulmi da majalisar masarautar, domin tunawa da rayuwa da wafatin babban malamin addinin Musulunci, kuma wanda ya assasa daular Usmaniyya, Sheikh Usmanu bin Fodiyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel