Usman Dan Fodio: Tauraro mai haskakawa a Afirika ta Yamma

Usman Dan Fodio: Tauraro mai haskakawa a Afirika ta Yamma

- Allah ya albarkaci Yankin Afirika ta Yamma da Manyan Malaman Addinin Musulunci wadanda su ka yada ilimi

- Cikin su akwai Shehu Usman Dan Fodiya wanda shi tauraro ne wanda ke haskaka yankin

- Dan Fodiyo shahararren malami ne a Afirika ta Yamma da ya yada ilimin da har ya zuwa yau a na amfana

Daya daga cikin abubuwa ma su ban sha'awa a cikin rayuwar musulmi na yankin Afirika ta Yamma shi ne yadda tarihin daular musulunci ya kunshi kyawawan dabi'un musulmi, da al'adun su, da kuma tsantsar bijirewar su ga turawan mulkin mallaka. Ba kowa ne ya san wadannan ababen sha'awa ba daga cikin wadanda ba 'yan yankin ba.

Hakazalika ba kowa ba ne ya san kyakkyawar tarihin ilimin addinin Musulunci a yankin Afirika ta Yamma, wanda har yanzun fafutuka da gwagwarmayar da magabata da su ka yada ilimin shi ne ke zaburar da musulmi wurin jajircewar su. Idan kuwa za a bayar da tarihin ilimin addinin musulunci a Afirika ta Yamma, to lallai sai an ambaci sunan Sheikh Uthman Bin Fodio Al-fulani, wanda a ka fi sani da Shehu Usman Dan Fodiyo.

KU KARANTA: Hukumar 'Yansanda ta kama kungiyar ma su garkuwa da mutane da satar shanu

An haifi Dan Fodiyo ne a tsakiyar karni na 18, a Arewacin Najeriya a yanzun. Ya hardace Al-Qur'ani ya na da karamin shekaru a wurin mahaifin sa da mahaifiyar sa. Daga nan sai ya samu ilimin hadisai daga malamai mabambanta har sai da ya kware kan manyan littafan hadisan nan guda 6. Ya kuma nemi ilimin harshen labarci har sai da ya gwanance. Dan Fodiyo kuma masani ne na ilimin Fassaran Al-Qur'ani, wato tafsiri.

Dan Fodiyo ya kasance mahukunci a mazhabar Imamu Malik alhalin kuma ya na da ilimi mai zurfi game da mazhabobin Shafi'i da Hanbali da Hanafi. Daga nan kuma sai ya zama jagora a darikar kadiriyya bayan ya hardace littafin Dala'ilul Khairati na Jazuli da Littafin Ahzab na Shazili.

Dan Fodiyo ya wallafa daruruwan littafai ma su dumbin yawa a kan fannoni daban daban na Musulunci wanda su ka hada da Hadisi, Fikihu na Malikiyya, Tauhidi da Wake. Yawancin littafan na sa da harshen Larabci ya rubuta su in banda kimanin guda 20 da ya rubuta su da yaren sa na Fillanci. Ya himmatu matuka wurin ilmantar da mata a yankin da ya zamanto Shugaba, Masarautar Sokoto a yanzun, wanda a hankali ta habaka har Kasashen Nijar da Burkina Faso.

Dukkan 'ya'yan sa 12 sun gaji ilimin sa, hatta 'ya'yan sa mata 2, a inda duk su ka zama manyan malamai. Ya kasance ya na bayar da karatun Hadisi da Fikihu da Tauhidi tsakanin La'asar da Isha'in kowace rana. Ya na kuma gabatar da karatu a kowani daren Juma'a wanda dumbin daliban sa maza da mata ke halarta. Dan Fodiyo ya kasance ya na mai maraba da mata game da neman ilimi ko tambaya a kan fikihu.

Shehu Usman Dan Fodiyo ya rasu ne a shekarar 1817 C.E. Dan sa Muhammad Bello shi ne ya gaje shi a fannin gwagwarmayar ilimi. Koda yake da dama daga cikin malaman Afirika ta Yamma da su ka zo bayan shi, ba su riske shi ba, amma sun riski rubuce-rubucen sa, sun karanta kuma sun amfana da su, sun kuma ji labarin sa. Allah ya ji kan magabata na kwarai. Mu kuma Allah ya bamu ikon amfanuwa da ayyukan su na kwarai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164