Coronavirus: Majalisar Wakilai ta kira Sadiya Umar kan rarraba kudin tallafin rage radadi

Coronavirus: Majalisar Wakilai ta kira Sadiya Umar kan rarraba kudin tallafin rage radadi

- Majalisar Wakilai ta kira Ministar Agaji da ci gaban Al'umma, Sadiya Umar Farouq

- Majalisar ta gayyaci Ministar ne dangane da kudaden da Kwamitin Fadar Shugaban Kasa na Musamman mai yaki da annobar korona wato PTF ya ba ta

- An nemi ministar ta bayyana a gaban kwamitin majalisar don ta yi bayanin yadda aka rarraba kudaden da aka bai wa ma'aikata da cibiyoyi da hukumomin da ke karkashin kulawarta

Majalisar Wakilai ta Najeriya, ta bukaci Ministar Agaji da jinkan Al'umma, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana a gabanta kan kudaden tallafin rage radadin annobar korona.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, Majalisar ta shigar da bukatar hakan ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuni.

Kwamitin lura da sha'anin al'umma na majalisar ya gayyaci Ministar ne dangane da kudaden da Kwamitin Fadar Shugaban Kasa na Musamman mai yaki da annobar korona wato PTF ya ba ta.

Sadiya Umar Farouq, Ministar Agaji da Ci gaban Al'umma
Sadiya Umar Farouq, Ministar Agaji da Ci gaban Al'umma
Asali: Twitter

An nemi ministar ta bayyana a gaban kwamitin majalisar don ta yi bayani dalla-dalla yadda aka rarraba kudaden da aka bai wa ma'aikatar da cibiyoyi da hukumomin da ke karkashin kulawarta.

A yayin da Ministar Agajin za ta bayyana a gaban Majalisar a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni, za ta amsa tambayoyi a kan sauran shirye-shiryen tallafi kamar irinsu N-Power da sauransu.

KARANTA KUMA: Za a gurfanar da mutumin da ya yi wa mata 40 fyade a Kano - Rundunar 'yan sanda

Wole Oke, wanda ke jagorantar kwamitin a majalisar, ya umarci duk jami’an shirin rarraba tallafi da abin ya shafa su bayyana a zahiri a gaban kwamitin tare da Ministar.

Oke ya jaddada cewa, rashin amsa wannan goron gayyata na kwamitin majalisar, zai haifar da sammacin cafke duk wanda ya juya musu baya.

Mista Oke ya kuma umarci jagoran Ofishin binciken kudi na kasa, Anthony Mkpe Ayine, ya bayyana a gaban majalisar.

Ya ce majalisar za ta bukaci Mista Ayine ya yi bayani dalla-dalla game da duk wani shige-da-fice na kudaden da aka batar yayin rarraba tallafin rage radadin annobar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel