Kwana Daya Bayan Ya Ci N1m, Dan Najeriya Ya Sake Lashe N2m A Cacar Da Ya Buga Da N5K

Kwana Daya Bayan Ya Ci N1m, Dan Najeriya Ya Sake Lashe N2m A Cacar Da Ya Buga Da N5K

  • Rayuwar wani matashi dan Najeriya ta sauya gaba daya bayan ya taki sa'a a gidan buga caca
  • Matashin ya lashe naira miliyan 2 a cacar da ya buga da N5k kacal, kwana daya bayan ya lashe naira miliyan 1
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga nasarar da mutumin da kalamai masu dadi yayin da wasu suka nemi tallafi daga gare shi

Kafar intanet ya kaure da murna bayan wani matashi ya sanar da batun nasarar da ya samu wajen lashe naira miliyan 2 a gidan caca.

Mutumin mai suna @AmakekeJohn ya wallafa tikitin da ke tabbatar da nasarar da ya samu a Twitter yayin da ya yi godiya ga wani mai suna @joysucex_ kan gudunmawar da ya bayar wajen nasarar da ya samu a cacar.

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Dan Shekaru 16 Ya Siya Dankareriyar Mota, Hotunan Sun Yadu

Gidan caca
Kwana Daya Bayan Ya Ci N1m, Dan Najeriya Ya Sake Lashe N2m A Cacar Da Ya Buga Da N5K Hoto: @AmakekeJohn, Pulse Gh
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa ya ci naira miliyan 1 a ranar da ta gabata.

"Jiya a nan ka ci mun naira miliyan 1, yau kuma ka ci mun wani naira miliyan 2. Gobe da izinin Allah, zan ci naira miliyan 50 daga cacar ka. Ka kware dan uwa."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hoton tikitin nasa ya nuna cewa N5k ya saka a cikin cacar.

Kalli wallafar tasa a kasa:

Jama'a sun yi martani a soshiyal midiya

@hannahojoh00 ta ce:

"Dan Allah, Dan Allah ka taimaka mun da dan wani abu don na biya kudin hayar gudana. N6ok ne kuma na haura wata daya ina karatu ne a Sokoto dan Allah."

@Baba89265046 ya ce:

"Nima haka zai faru da ni...Miliyoyina za su zo kafin Janairu."

@AkanjiwasiuAbi1 ya ce:

"Na tayaka murna maigida. A dan bani wani abu na sa a aljihu."

Kara karanta wannan

Nagode Mama: Aminu Adamu ya Bada Hakuri a Fili, Yayi Alkwari Zai Gyara Halinsa

@Joe_Akpanke ya ce:

"Woaww a ina kuke ganin wannan cacar ne."

@ElfMacarthy ya ce:

"Na ga cacar amma babu kudin bugawa, talauci yayi kyau. Bari na ci gaba da tafi da taya wadanda suka yi nasara murna har sai ranar da abun ya kai kaina..."

Matashi ya yi godiya ga Allaha a masallaci bayan ya lashe makudan kudade a caca

A wani labarin kuma, wani matashi ya lashe zunzurutun kudi har naira miliyan 38 a wani wasan caca da ya buga.

Jim kadan bayan ya yi nasara, sai aka gano matashin yana alwala tare da shiga masallaci domin godiya ga Ubangiji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel