Duk da Miliyoyin da Ake Biyansu, NILDS Ta ce Kudin Aikin ‘Yan Majalisa Ya Yi Kadan

Duk da Miliyoyin da Ake Biyansu, NILDS Ta ce Kudin Aikin ‘Yan Majalisa Ya Yi Kadan

  • Shugaban cibiyar NILDS ya yi kira a karawa ’yan majalisa kudi domin su iya aikin sa idanu a kwamitocin majalisa
  • Farfesa Abubakar Sulaiman ya fadawa kungiyar manema labarai idan kwamitoci ba su da kudi, toba za ayi gaskiya ba
  • An kafa cibiyar NILDS ne domin yin nazarin ayyukan Majalisa da gyara Dimokuradiyyar kasa a shekarar 2011

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Cibiyar NILDS mai nazarin ayyukan Majalisa da Dimokuradiyya ta Najeriya ta na so a kara yawan kudin da ake biyan ’yan majalisa.

Daily Trust ta ce shugaban NILDS na kasa, Farfesa Abubakar Sulaiman ya bukaci da ya ke jawabi da ya karbi bakuncin kungiyar ‘yan jarida.

'Yan Majalisar Tarayya
NILDS ta ce a kara kudin 'Yan Majalisar Tarayya Hoto: @HouseNgr
Asali: Facebook

NILDS ta koka kan kalubalen da ta ce ‘yan majalisa su na fuskanta wajen aikinsu.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira Biliyan 1.5 wajen sayo motocin uwargidar Shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai da kudi majalisa za ta yi aikin kwarai

Farfesa Sulaiman ya ke cewa idan ana so shugabannin kwamitocin majalisa su ji dadin yin aiki da kyau, wajibi a ware masu isassun kudi.

A lokacin da ake rabawa 'yan majalisa motoci, sai ya ce samun kudi mai tsoka ne zai ba wakilan mutane ikon aiki babu tsoro ko neman alfarma.

Tsarin mulkin kasa ya ba majalisa damar kawo dokoki da yi wa dokokin baya kwaskwarima da sa ido a ayyukan bangaren zartarwa.

Majalisa: Mutane ba su son maganar - NILDS

Abubuwa ba za su gyaru ba sai ‘yan majalisa sun samu kudin da su ke bukata, Farfesan ya ce jama’a ba su son jin an fadi wannan magana.

Sulaiman ya na da ra’ayin cewa sai gwamnati ta na biyan ‘yan majalisa da kyau sannan kwamitocinsu za su yi aiki da gaskiya da rikon amana.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen gwamnoni da suka yi wa iyayen gidansu a siyasa karan-tsaye

“Idan ‘yan majalisa za su duba ayyukan NPA, NIMASA da NNPCL, abin da ake ware masu N3m ne a hukumar da ke harkar tiriliyoyi.
Kuma sai ku ce ba za su fuskanci barazana ba? Mu na yaudarar kan mu ne kurum.”

- Farfesa Abubakar Sulaiman

Jide Oyekunle wanda ya jagoranci tawagar manema labaran ya yabawa aikin cibiyar saboda irin kokarinsu na horar da ‘yan jarida a kasar nan.

Tinubu ya gargadi wadanda aka ba mukami

Bola Ahmed Tinubu ya na so duk wanda ba zai iya aiki da kyau da shi ba, ya yi murabus daga matsyainsa kamar yadda aka samu labari.

Yanzu haka ana taron bita da aka shiryawa Ministoci, hadimai da manyan gwamnati, Bola Tinubu ya gabatar da jawabi a raron farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng