Majalisar Dattawa Ta Amince da Naɗin Mutane 7 Daga Cikin 10 da Shugaban Tinubu Ya Naɗa a Muƙamai
- Bakwai daga cikin sabbin kwamishinonin hukumar zabe ta ƙasa INEC da Bola Tinubu ya naɗa sun tsallake tantancewa a majalisa
- Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin da shugaban ƙasa ya musu a zaman ranar Laraba, an gano abinda ya sa ba a tabbatar da sauran 3 ba
- A makon da ya wuce ne shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin RECs 10 waɗan da zasu jagoranci INEC a matakin jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja -Majalisar dattawan Najeriya ta aminece da mutane 7 cikin 10 waɗanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin REC.
Channels tv ta ruwaito cewa majalisar ta fara aikin tantance wa da tabbatar da naɗin sunayen waɗan da Tinubu ya naɗa kwamishinonin hukumar zaɓe (INEC) watau RECs.
Mutane 7 daga cikin mutane 10 sun tsallake kuma Sanatocin sun amince da naɗinsu yayin da sauran ragowar ukun kuma ba su halarci zauren majalisar ba a yau Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin kwamishinonin INEC da majalisa ta tabbatar da su
Waɗan da majalisar dattawan ta tabbatar da naɗinsu a matsayin kwamoshinonin INEC sun haɗa da Mista Etekamba Umoren daga Akwa Ibom da Mista Isha Ehimeakne daga Edo.
Sauran sun ƙunshi Barista Oluwatoyin Babalola daga Ekiti, Mista Abubakar Ahmed daga Gombe, Shehu Wahab daga Kwara; Aminu Idris daga Nasarawa da kuma Mohammed Abubakar Sadiq daga Neja.
Bola Tinubu ya aika sako tun farko
Wannan tabbatarwa na zuwa ne bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tura sako ga majalisa yana mai rokon ta amince da naɗin sabbin RECs ɗin INEC.
Shugaba Tinubu ya buƙaci tabbatar da naɗe-naɗen bisa tanadin sashi na 154(1) da ke ƙunshe a kundin tsarin mulkin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
Idan baku manta ba a makon da ya shuɗe, Bola Tinubu ya amince da naɗin sabbin kwamishinonin zaɓe waɗanda su ne shugabannin INEC a matakin jihohi, za su shafe zango ɗaya na shekaru biyar.
Masu zanga-zanga sun mamaye majalisa
A wani rahoton na daban masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya a Najeriya sun fita tattaki da zanga-zangar lumana zuwa majalisar tarayya da ke Abuja.
Masu zanga-zangar sun nemi a gaggauta tsige ƙaramin ministan tsaron Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara , Bello Matawalle.
Asali: Legit.ng