Gungun Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Zauren Majalisar Tarayya, Sun Nemi a Tsige Minista 1 Rak
- Wasu ƴan gwagwarmaya sun mamaye majalisar dokokin tarayya suna neman a tsige ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle
- Masu zanga-zangar sun buƙaci shugaban majalisar dattawa ya takura wa shugaban ƙasa ya sauke Matawalle daga muƙaminsa
- A cewarsu, suna zargin tsohon gwamnan yana da alaƙa da ƴan bindiga da suka addabi mutane
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Daruruwan masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya a Najeriya sun fita tattaki da zanga-zangar lumana zuwa majalisar tarayya da ke Abuja ranar Laraba.
Masu zanga-zangar sun nemi a gaggauta tsige ƙaramin ministan tsaron Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Masu zanga-zangar a harabar zauren majalisar sun riƙa rera waƙoƙin haɗin kai kana suka ɗaga tutoci masu rubutu daban-daban kamar, "A kori Bello Matawalle yanzu."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka sun ɗaga allon da ke ɗauke da rubutun, "Kuɗin tsaron mu ba su da tsaro." da sauran makamantansu, kamar yadda Vanguard ta ruqaito.
Daga cikin sauran abubuwan da suka nuna damuwa, masu zanga-zangar karkashin kungiyar Civil Society Advocacy Groups for Accountability and Probity sun zargi Matawalle da, "ɗasawa da ƴan bindiga."
Sun aike da sako ga Akpabio
Jagoran tawagar masu zanga-zangar, Danesi Momoh, ya yi jawabi ga ƴan jarida a gaban majalisar, inda ya tura sako ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Ya yi kira ga shugaban majalisar dattawa ya matsa wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, lamba domin ya sauke Matawalle daga muƙaminsa.
A kalamansa ya ce:
"Tsarin tsaro da ɗora jagora mara inganci na ɗaya daga cikin kuskuren wannan gwamnatin, amma za a iya gyara kuskuren idan majalisar dattawa ta ɗaga murya ta hanyar da ta dace."
"Muna kira ga Majalisar Dattawa ta tashi tsaye ta tabbatar da an tsige shi cikin gaggawa domin dawo da fatan ƴan Najeriya na samun shugabanci na gari."
Da yake martani kan zanga-zangar, Darakta a Majalisar ta kasa, Salihu Abdullahi, wanda ya karbi takardar koken a madadin Akpabio, ya nuna jin daɗin yadda aka yi zanga-zangar cikin lumana.
Ya kuma yai musu alkawarin cewa zai miƙa dukkan koken da suka gabatar da waɗan da ya dace.
Bam.ya tashi a Yobe
A wani rahoton kuma Akalla mutanen kauye 20 ne suka rasa rayuwarsu yayin da wani babur ya tashi da bam din da kungiyar Boko Haram ta dasa a jihar Yobe.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen sun dawo daga makokin matasa 17 da aka kashe a yankin ƙaramar hukumar Gaidam ranar Litinin, lokacin da Bam ɗin ya tashi.
Asali: Legit.ng