Wani Fasto Mai Tsala-Tsalan Mata 2 Kuma Yake Shirin Auren Ta 3 Ya Hakura, Ya Fadi Dalili
- Wani fasto da ke da matan aure fiye da daya ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya yi karin haske game da shirinsa na auren mata ta uku
- Yan watanni da suka gabata, faston wanda ya mallaki matan aure biyu da yara da yawa, ya sanar da shirinsa na kara aure
- Jama'a sun yi martani kan sauya shawara da ya yi yayin da mutane da dama basu so hakan ba, wasu kuma sun yi maraba da ci gaban
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani faston kasar Botswana mai suna Sekati Kemmonye, ya canja shawara game da shirinsa na auren mata ta uku.
A wata wallafa da ya yi a shafin Facebook a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, Fasto Sekati ya bayyana cewa ya gama auren sannan ya ba yan matan da ke muradin zama matansa ta uku da su yi hakuri.
Dalilin da yasa Sekati ya hakura da auren mata ta uku
Kamar yadda Sekati ya bayyana, matansa biyu sun fahimci juna sosai kuma suna iya bakin kokarinsu don tabbatar da alaka mai kyau a tsakaninsu kuma wannan ne yasa ya yanke shawarar tsayawa a mata biyu kawai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"NA GAMA.
"Ina ganin duba da yadda matana suke zaman lafiya, da kuma kokarin da suka yi don samun irin wannan kyakkyawar dangantaka, abun da ya fi mun kawai in tsaya a nan!
"Ga wadannan yan mata da matayena suke ta tattaunawa da su a matsayin wadanda zan aura, ina mai ba ku hakuri.
"Akwai mazajen kirki a waje wadanda ke da niyan auren mace daya wadanda za su so ku, ku kadai!
"Nagode."
Sekati ya ce komai ya ji zam a gidansa
Magidanci wanda ya tara yara da yawa ya jaddada cewar iyalinsa sun tara komai, yana mai cewa duk wanda ya iya rawa ya san lokacin barin filin taro.
Jama'a sun yi martani kan shawarar faston
Oaitse Switch Sekgwama ya ce:
"Kamar yadda na fadi, mafi karancin shine mata 3. Saboda haka, ban san me yasa The Sekatis ya sauya tsarin a amma sami bai dace ba."
Gladys Bosa Dingake Gabohole:
"Da fatan kana fadin wannan har zuciyarka ne! a'a ⛔️⛔️⛔️⛔️⛔️ga mata ta 3."
Tshegofatso Joy Dikomane ta ce:
"A matsayina na mata ta 3, abun ya yi mun ciwo sosai."
Fasto ya halasta auren mata da yawa
A wani labarin, mun ji cewa wani limamin coin Anglican da ke Nnewi jihar Anambra, Rev Ogbuchukwu Lotanna, ya sauka daga kujerarsa.
Rev Lotanna, yace ya samu sabon wahayi na ya kwadaitawa mutane auren mace fiye da daya don a rage zinace-zinace cikin al'umma.
Asali: Legit.ng