Da Dumi-Dumi: Jami'an Tsaro Sun Cafke Shugaban Kungiyar NLC, An Bayyana Dalili
- Shugaban kungiyar kwadago, NLC Joe Ajaero ya shiga hannun 'yan sanda a birnin Owerri da ke jihar Imo a yau Laraba
- 'Yan sanda ne dauke da makamai su ka cafke Ajaero a sakatariyar kungiyar da ke birnin Owerri
- Daraktan yada labarai ba kungiyar, Upper Benson shi ya bayyana haka a yau Laraba ga manema labarai
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Imo - Jami'an tsaro sun kama shugaban Kungiyar Kwadago (NLC), Joe Ajaero a Owerri babban birnin jihar Imo.
Daruruwan jami'an 'yan sanda dauke da makamai sun kama Ajaero ne a sakatariyar kungiyar inda su ka tafi da shi.
Mene dalilin kama shugaban NLC?
Daraktan yada labarai na kungiyar, Benson Upper shi ya bayyana haka ga gidan talabijin na Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce lamarin ya faru ne a yau Laraba 1 ga watan Nuwamba a birnin Owerri da ke jihar Imo.
Legit ta tattaro cewa an kama Ajaero ne yayin gudanar da wata zanga-zanga a jihar.
Wasu bata gari na amfani da zanga-zangar wurin barnata dukiyoyin al'umma da sace-sace.
Ina aka kai shugaban NLC?
Sai dai har zuwa yanzu da ake hada wannan rahoto ba a san inda jami'an tsaron su ka wuce da Ajaero.
Yayin sanar da kamun Ajaero, daraktan yada labarai na kungiyar, Upper Benson ya ce an kama Ajaero ne a sakatariyar kungiyar da ke birnin Owerri.
Ya ce:
"An kama shugaban kungiyar kwadago ta NLC a yau a harabar sakatariyar kungiyar a Owerri, jami'an tsaro ne su ka dauke shi, ba a san inda su ka kai shi ba."
NLC ta yi fada da ministan Tinubu
A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta NLC, ta bayyana cewa ba za ta yi zama da Gwamnatin Tarayya ba idan ministan kwadago ya halarta.
Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka inda ya ce ba ya bukatar Simon Bako Lalong a zaman.
Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar ke ci gaba da zama da Gwamnatin Tarayyar don samun daidaito da matsaya kan yajin aiki.
Asali: Legit.ng