"Mun Shirya": Rabiu Ya Gaya Wa Tinubu Sabon Farashin Siminti, Yayin da Yan Kasuwa Ke Siyarwa a N5000
- Attajiri na biyu a Najeriya, Abdulsamad Rabiu, a ƙarshe ya mayar da martani ga ƴan kasuwa da suka ki sayar da simintinsa na BUA a kan N3,500
- Ƴan Najeriya sun yi farin ciki da suka ji batun rage farashin buhun simintin, sai dai murnarsu ta koma ciki lokacin da suka je kasuwanni suka tarar ba haka zancen yake ba
- Kamfanin simintin BUA na Rabiu na ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke samar da siminti, tare da kamfanin Dangote da Lafarge
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu, ya tabbatar da cewa kamfaninsa na siminti ya rage farashin simintinsa daga Naira 4,500 zuwa Naira 3,500 kan kowane buhu.
Ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan wata ganawar sirri da ya yi da shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja, a ranar Talata, 31 ga watan Oktoban 2023.
Rabiu ya yi nuni da cewa tattaunawar da suka yi dangane da farashin siminti wani bangare ne na tattaunawarsa da shugaban ƙasa Bola Tinubu, cewar rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
BUA ya rage farashin buhun siminti
A kalamansa:
"An rage farashin simintin BUA daga Naira 4,500 zuwa Naira 3,500 kan kowane buhu, abin yana faruwa, a magana ta gaskiya, na tattauna batun siminti da shugaban ƙasa."
"Muna da sabbin wurare biyu da za mu fara aiki, in Allah ya yarda, nan da ƙarshen shekara. Shugaban ƙasa ya amince ya zo ya ƙaddamar da ɗaya daga cikin wuraren da za a yi a Sokoto a watan Janairu, in Allah Ya yarda kuma da haka za mu samu ƙarin abin da mu ke samarwa."
"Kuma da zarar hakan ta faru, farashin siminti zai ragu, fiye da yadda farashinsa yake a faɗin ƙasar nan, kuma a shirye muke mu yi hakan, a shirye muke mu bayar da goyon baya."
Rabiu ya ƙara da cewa:
"Idan aka yi duba kan sana'ar da muke ciki yanzu, sana'ar siminti, kusan kaso 80% na dukkanin abin da muke buƙata domim samar da siminti muna da shi a Najeriya, irin hakan muke buƙata domin ƙarfafa gwiwar yin haƙar ma'adanai, noma saboda muna da ƙasa, muna da mutane, muna da yanayi mai kyau da ruwa."
Abdulsamad Ya Ci Ribar N1bn
A baya rahoto ya zo cewa a cikin sa'o'i 24, mamallakin kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu, ya ci ribar N1bn a cikin sa'o'i 24 kacal.
Hamshaƙin attajirin ya samu wannan gagarumar ribar ce wavce ta sanya ƙara sama a cikin jerin attajiran duniya inda ya koma na 403.
Asali: Legit.ng