Yan Boko Haram Sun Yi Ajalin Matasa 17 Saboda Kin Biyan Haraji, Sun Tura Sakon Gargadi

Yan Boko Haram Sun Yi Ajalin Matasa 17 Saboda Kin Biyan Haraji, Sun Tura Sakon Gargadi

  • ‘Yan Boko Haram sun yi ajalin wasu matasa guda 17 a jihar Yobe saboda sun ki biyan kudin haraji
  • Maharan sun durfafi kauyen Gurokayeya da ke karamar hukumar Geidam a jihar tare da hallaka matasan
  • Tun farko sun zabi wasu matasa 21 masu shekaru 20 zuwa 30 tare da harbesu inda nan take 17 su ka mutu

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Yobe – Mayakan Boko Haram sun hallaka wasu matasa 17 saboda sun ki biyan kudin haraji a jihar Yobe.

Lamarin ya faru ne a kauyen Gurokayeya da ke karamar hukumar Geidam da ke jihar saboda kin biyan haraji daga matasan.

Boko Haram sun kashe matasa 17 kan biyan haraji a Yobe
Boko Haram sun hallaka matasa 17 kan haraji a Yobe. Hoto: Mai Mala Buni.
Asali: UGC

Mene dalilin Boko Haram na kisan matasan a Yobe?

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ajalin babban mai sarautar gargajiya, sun sace matarsa, dansa da wasu mutum 8

Daily Trust ta tattaro cewa maharan sun durfafi kauyen ne da misalin karfe 10 na dare inda su ka tara dukkan mutanen kauyen a wuri daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan mu su jawabai sun fara hukunta su inda su ka zabi wandanda za su kashe tare da yin ajalinsu.

Wata majiya ta tabbatar da cewa maharan sun zabi matasa 21 da su ke da shekaru tsakanin 20 zuwa 30 tare da harbesu.

Har ila yau, maharan sun kuma bar tsofaffi da yara kanana ba tare da yi mu su komai ba, matasa 17 daga ciki sun mutu nan take.

Wane gargadi Boko Haram su ka bai wa matasan?

Cewar majiyar:

“Sun zabi matasa ma su shekaru 20 zuwa 30 inda su ka harbe su nan take yayin da su ka bar mata da yara kanana.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban karamar hukuma a Benue bayan sace shi na kwanaki

“Matasa 17 din sun mutu nan take yayin da aka kwashi sauran mutum hudu zuwa asibiti cikin mawuyacin hali.”

Majiyar ta kara da cewa ‘yan Boko Haram din sun dauki matakin ne bayan yin gargadi a lokuta da dama na cewa ‘yan kauyen su biya haraji amma a banza.

Bayan kisan matasan, maharan sun kuma mu su gargadi mai tsauri dangane da kin biyan kudin haraji kafin su bar wurin.

Sojoji sun hallaka kwamandan ‘yan bindiga a Kebbi

Kun ji cewa, sojoji sun yi ajalin wani kwamandan ‘yan bindiga mai suna Mainasara a jihar Kebbi.

Rundunar ta samu wannan nasara ce bayan samun bayanan sirri daga jama’a kan ayyukan ‘yan ta’addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.