Ma'aikata, Wike da Sauran Mutanen da Za Su Amfana da N2.1tr da Tinubu Zai Kashe
- Bola Ahmed Tinubu ya na so majalisar tarayya ta amincewa gwamnatinsa kashe karin N2,176,791,286,033 a kasafin kudin bana
- Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Abubakar Bagudu ya yi bayanin yadda gwamnatin tarayya za ta batar da biliyoyin kudin
- Gyaran manyan gadoji da biyan karin albashi da aka yi wa ma’aikata saboda canjin farashin fetur za su ci N510, 000, 000, 000
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisar tarayya takarda domin a amince masa kashe N2,176,791,286,033 a shekarar nan ta 2023.
Rahoton da aka samu a tashar Channels TV ya nuna idan an amince da kwarya-kwaryar kasafin, za a batar da kudin a wasu aikace-aikace.
Daga cikin karin da za ayi a kasafin kudin banan za a batar da N605b a kan sha’anin tsaro domin a biyawa jami’an tsaro bukatun da su ka taso.
Za ayi gyaran gadoji a kasafin 2023
A cikin kwarya-kwaryar kasafin kudin, an warewa wasu hukumomi N18,0000,000,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Nation ta ce za a kashe N992,802,015,985 wajen sallamar ma’aikata hakokinsu a cikon kasafin, wannan adadi ya wakilci 45% na kudin.
N300, 000, 000, 000 za su kare a gyaran gadoji da ma’aikatar ayyuka za ta kashe a fadin Najeriya.
Karin albashin ma'aikata zai ci N210bn
A sakamakon karin albashin da aka yi wa ma’aikatan gwamnatin tarayya saboda tashin farashin da fetur ya yi, za a kashe karin N210bn.
Sababbin ma’aikatu irinsu harkokin ruwa da sauransu da aka kirkiro a lokacin da Bola Tinubu ya nade Ministoci za su ci N8, 000, 000, 000.
Akwai zabukan gwamnonin jihohi da hukumar INEC za ta shirya a Kogi, Bayelsa da Imo, sai yanzu ne ake ware masu N18, 000, 000, 000, 000.
Gwamnati ta ware N400, 000, 000, 000 da za a rabawa talakawa domin a rage radadi da kuma N200, 000, 000, 000 a kan kayayyakin gona.
Kwangilolin da za a aiwatar a karkashin hukumar FCTA a Abuja za su ci N200, 000, 000, 000, fadar shugaban kasa za ta ci N28, 000, 000, 000.
Su wanene za su amfana da kasafin?
1. Ministan Abuja (FCTA)
2. Gboyega Oyetola
3. Hannatu Musawa
4. Ma’aikatan gwamnati
5. Hukumar NSIPA
6. Ma’aikatar tsaro
7. Ma’aikatar boma
8. David Umahi (Ayyuka)
9. Hukumar INEC
10. Aso Rock
$1 ta koma N1100 a kasuwar canji
Da alama za a samu saukin farashin kayan kasashen waje saboda faduwar Dala, ana da labari kudin Amurkan ya sauka daga N1300 zuwa N1100.
Wani ‘dan canji ya shaidawa manema labarai cewa Dala ta na dawowa kasuwa sannu a hankali, yanzu su na ganin Dalar Amurka sosai.
Asali: Legit.ng