Mayakan Boko Haram Sun Salwantar da Rayukan Mutum 16 a Wani Sabon Hari a Jihar Yobe
- Ƴan ta'addan Boko Haram sun halaka mutum 16 mafiya yawansu matasa a wani ƙazamin hari da suka kai a jihar Yobe
- Miyagun ƴan ta'addan sun kai harin ne a ƙauyen Nguro Kayayya na ƙaramar hukumar Geidam ta jihar
- Hukumomi sun tabbatar da aukuwar harin tare da tura jami'an sojoji domin dawo da zaman lafiya a yankin
Jihar Yobe - Aƙalla mutum 16 ne waɗanda mafiya yawansu matasa ne aka kashe, yayin da wasu mutum huɗu suka samu raunuka bayan wani sabon hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ƴan ta'addan sun mamaye ƙauyen Nguro Kayayya da ke wajen ƙaramar hukumar Geidam da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Litinin, 30 ga watan Oktoban 2023.
Yadda harin ya auku
Wani majiya wanda yake da ƴan uwa a ƙauyen ya bayyana cewa ya ƙirga gawarwakin mutum 16 bayan harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Sun kai hari ƙauyen ne a lokacin da yawancin mazauna garin ke barci. Na je garin domin na ganewa idona, kuma na ƙirga gawarwaki 16 yayin da mutum huɗu suka samu raunuka. Waɗanda suka samu raunukan ana duba lafiyarsu a asibitin kwararru da ke Geidam.”
Ya ce ƴan ta'addan sun kai hari ƙauyen ne bayan mazauna yankin waɗanda akasari manoma ne suka ƙi biyan harajin da mayakan suka ɗora musu.
Babagana Aisami Geidam, wani mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama ya bayyana cewa kawo yanzu mutum 16 ne suka mutu yayin da wasu mutum uku suka samu raunuka, inda ya ce mutum ɗaya na cikin mawuyacin hali.
Ya ce an yi jana'izar mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inda ya ce an tura jami'an sojoji zuwa ƙauyen.
Menene martanin hukumomi kan harin?
Da aka tuntubi mataimakin daraktan hulɗa da jama'a na rundunar Operation Lafiya Dole, Kyaftin Muhammad Shehu, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ƴan ta’addan sun yi zargin cewa mutanen ƙauyen na bayar da bayanai ga sojoji domin fatattakarsu.
A kalamansa:
"Ƴan sun farmaki mutanen ƙauyen ne saboda zargin cewa suna taimaka mana da bayanai masu amfani domin murƙushe su."
"Ba zan iya bayar da cikakken adadin waɗanda suka mutu ba, amma abin da na sani shi ne an tura jami'an sojoji sannan an dawo da zaman lafiya."
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin garin Geidam mai suna Ahmed Maigari, wanda ya yi magana kan yanayin tsaro a yankin.
Maigari ya bayyana cewa an samu sauƙin hare-haren ƴan Boko Haram a yankin, inda ya ce ba su cika taɓa mutane ba, sai waɗanda suka takura musu.
Ya bayyana cewa ƴan ta'addan na yin fako kan waɗanda ke bayar da bayanan ayyukansu ga jami'an tsaro sannan su kawo musu farmaki.
Mayakan Boko Haram Sun Halaka Babban Limami
A wani labarin kuma, mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram sun halaka wani babban limami a jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun kai farmaki a gidan babban limamin Kaga da ke Malamti, a wajen garin Benishek, inda suka halaka shi tare da wani ɗan sakai mutum ɗaya.
Asali: Legit.ng