Kotun Koli Ta Cimma Matsaya Kan Karar Neman a Tsige Gwamna Uzodinma Na APC

Kotun Koli Ta Cimma Matsaya Kan Karar Neman a Tsige Gwamna Uzodinma Na APC

  • Kotun ƙoli ta cimma matsaya kan ƙarar da jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta shigar tana neman a tsige gwamna Hope Uzodinma
  • Kotun ƙolin ta cimma matsayar ɗage fara sauraron ƙarar har zuwa ranar 5, ga watan Disamban 2023
  • Bayan shekara uku da shigar da ƙarar, kotun ta sanya ranar Talata, 31 ga watan Oktoba domin fara sauraron ƙarar amma daga baya ta sauya ranar

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ƙoli ta ɗage sauraron ƙarar da jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta shigar na neman a tsige Hope Uzodinma daga muƙamin gwamnan jihar Imo zuwa ranar 5 ga watan Disamba.

Kotun ƙolin ta sanya ranar Talata 31, ga watan Oktoban 2023, domin fara sauraron ƙarar wacce jam'iyyar APGA ta shigar.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Bayelsa: Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan matsayin takarar Timipre Sylva na APC

Kotun koli ta dage sauraron karar neman tsige Hope Uzodinma
Kotun koli ta dage sauraron karar neman tsige gwamna Hope Uzodinma Hoto: @Hope_Uzodinma1
Asali: Twitter

Jam'iyyar APGA a shekarar 2020 ta shigar da ƙara inda jam’iyyar ta ce ya kamata a sake yin wani sabon zabe a jihar bayan da kotun ƙoli ta soke zaɓen ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Emeka Ihedioha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ta ce kotun ƙoli ba ta yanke hukunci kan sahihancin takarar Uzodinma ba tunda Ihedioha da PDP ba su ƙalubalance ta ba a ƙarar da aka shigar mai lamba SC/1462/2019.

Bayan shekara uku kotu za ta fara sauraron ƙarar

Shekaru uku bayan shigar da ƙarar, kotun kolin ta sanya ranar Talata, 31 ga watan Oktoban, a matsayin ranar fara sauraron ƙarar.

Sai dai a lokacin da ƴan jarida suka ziyarci kotun kolin a ranar Talata, ba a sanya batun cikin jerin ƙararrakin da kotun za ta saurara ba, rahoton The Punch ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Kungiyar kwadago ta ba gwamnatin tarayya sabon sharadi domin halartar zaman da za su yi

Ɗaya daga cikin rajistarorin kotun ƙolin ya shaidawa manema labarai cewa an ɗage ƙarar zuwa ranar 5, ga watan Disamban 2023.

Shettima da Gwamnonin APC Sun Dira Imo

A wani labarin kuma, mataimakin shugabana ƙasa, Kashim Shettima, da wasu gwamnonin jam'iyyar APC, sun dira a jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Mataimakin shugaban ƙasar ya isa jihar Imo ne tare da tawagarsa domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamna Hope Uzodinma mai neman yin tazarce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng