Kano: Hukumar Hisbah Ta Cafke ’Yan Daudu Guda 8 Su Na Tika Rawar da Badala a Wurin Biki

Kano: Hukumar Hisbah Ta Cafke ’Yan Daudu Guda 8 Su Na Tika Rawar da Badala a Wurin Biki

  • Hukumar Hizbah ta kama ‘yan daudu guda takwas yayin wani biki a jihar Kano
  • Hukumar ta ce ta samu rahoton ne daga wasu mutane inda ta yi tattaki zuwa wurin
  • Mataimakin daraktan hukumar, Dakta Mujaheed-Aminudden shi ya bayyana haka a yau Talata

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar KanoHukumar Hisbah a jihar Kano ta cafke wasu ‘yan dauda guda takwas yayin da su ke tikar rawa a Kofar Waika da ke karamar hukumar Gwale.

An kama ‘yan daudun ne yayin da su ke tikar rawa a wani bikin uban gidansu wanda wasu mutane su ka kai rahotonsu ga hukumar.

Hisbah ta cafke 'yan daudu guda 8 a su na badala a jihar Kano
Hisbah ta yi nasarar kwamushe wasu 'yan daudu a Kano. Hoto: Hisbah Command.
Asali: Facebook

Yaushe Hisbah ta kama ‘yan daudun a Kano?

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ajalin babban mai sarautar gargajiya, sun sace matarsa, dansa da wasu mutum 8

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin kwamandan hukumar, Dakta Mujaheed Aminudden-Abubukar ya fitar a yau Talata 31 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mujaheed ya ce sun samu rahoton shaidancin ne daga wasu mutane cewa wasu sun yi shigar mata da kayan Fulani su na tika rawar a biki, Daily Nigerian ta tattaro.

Ya ce bayan samun rahoton, jami’ansu sun kai farmaki wurin bikin inda su ka yi nasarar kama takwas daga cikinsu da kuma angon wanda shi ma ya yi shigar mata.

Ya ce:

“Mun samu rahoton yayin da jami’anmu su ka halarci wurin daurin auren inda su ka kama mutane takwas daga ciki.
“Daga cikin wadanda aka kaman akwai angon wanda shi ma ya yi shigar mata da kayan Fulani inda ya ke tikar rawa.”

Wane mataki Hisbah ta dauka kan ‘yan daudun?

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya ba da umarnin tantance karin mutane 147 don auren gata, ya bayyana matakin gaba

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun tabbatar da aikta laifukan bayan gurfanar da su a gaban kotun shari’ar Musulunci.

Wadanda ake zargin sun nema ayi mu su sassauci yayin yanke hukunci a gaban kotun, cewar Premium Times ta tattaro.

Mai Shari’a, Khadi Tanimu-Sani ya ba da umarnin bai wa ko wannensu bulali 10 tare da biyan naira dubu 20.

Ya kuma umarci ko wannensu ya kawo wanda zai tsaya masa ko kuma a kulle shi a gidan gyaran hali na tsawon watanni uku.

Abba Kabir ya umarci tantance mutum 147 don auren gata

A wani labarin, Gwamnan Abba Kabir ya umarci tantance karin mutane 147 don yi mu su auren gata a jihar.

Gwamnan ya dauki nauyin aurarraki 1,800 a kwanakin baya wanda aka gudanar a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.