Yan Sanda Sun Cafke Daliban Firamare 2 da Cinna Wa Makarantarsu Wuta, an Bayyana Yadda Abin Ya Faru

Yan Sanda Sun Cafke Daliban Firamare 2 da Cinna Wa Makarantarsu Wuta, an Bayyana Yadda Abin Ya Faru

  • Jami’an ‘yan sanda sun cafke daliban firamare guda biyu da su ka kona makarantarsu kurmus da wuta a jihar Ogun
  • Kakakin rundunar a jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da kama yaran inda ta ce yanzu haka ana kan bincike
  • Idan ba a manta ba a ranar 29 ga watan Oktoba yaran ma su suna Wahid Musa da Malik Iliasu su ka cinna wa makarantar wuta

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun – Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta cafke daliban firamamre kan zargin cinna wa makarantarsu wuta.

Daliban firamaren ma su na Wahis Musa mai shekaru shida da Malik Iliasu mai shekaru tara sun cinna wa makarantar al’umma wuta da ke Isheri Olofin a karamar hukumar Ifo da ke jihar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi ajalin kasurgumin kwamandan 'yan bindiga, Mainasara da wasu 2 a jihar Arewa

'Yan sanda sun cafke daliban firamare kan cinna wa makaranta wuta
Daliban firamare sun shiga hannu kan zargin kona makaranta a Ogun. Hoto: NPF Ogun.
Asali: Facebook

Me ake zargin daliban firamaren da aikatawa?

Kakakin rundunar a jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da kama yaran inda ta ce sun aikata haka a ranar 29 ga watan Oktoba, Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta:

“Biyu daga cikin daliban makaratar al’umma da ke Isheri Olofin Wahid Musa da Malik Iliasu su na hannun ‘yan sanda.
“Ana zargin yaran makarantar firamaren da cinna wa makarantar wuta a ranar 29 ga watan Oktoban wannan shekara.”

Wane mataki aka dauka kan daliban firamaren?

Ta kara da cewa sun sa mu rahoton faruwar lamarin ne daga wani mai sarauta a yankin inda ya sanar da jami’ansu abin da ke faruwa.

Ta ce ya bayyana mu su cewa Musa da Iliasu sun shiga cikin daya daga cikin dakunan karatu inda su ka tara littattafai da kona su kurmus.

Kara karanta wannan

Daga Yin Barazanar Tsige Gwamna, Majalisar Dokoki ta Kama da Wuta Cikin Dare a Ribas

Odutola ta ce an fara bincike mai zurfi kan lamarin inda ta ce su na neman iyayen yaran don sanin matakin da za su dauka, cewar Vanguard.

Kakakin rundunar ta bayyana aikata wannan laifi a wurin yara kanana kamar wadannan abin takaici wanda ke bukatar nazari sosai.

An cafke Fasto da kokon kan dan Adam a Ogun

A wani labarin, jami’an ‘yan sanda sun cafke wani Fasto da wasu mutane uku kan zargin mallakar kokon kan dan Adam.

An tasa keyar Fasto ne zuwa ofishin ‘yan sanda da sauran wadanda ake zargin don fuskantar hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.