Bidiyon Jami’ar Yar Sanda Tana Rera Taken Kasa Cike Da Kura-kurai Ya Girgiza Intanet
- Wata jami'ar yar sanda ta haddasa cece-kuce a gari bayan ta rera wakar taken kasa cike da kura-kurai
- Abun takaicin ya faru ne a wani taron manyan jami’an yan sanda wanda ya gudana a kan idon gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma da sauran manyan masu fada aji
- Yan Najeriya sun yi martani ga bidiyon da ya yadu inda mutane da dama suka tambayi ko akwai abun da ya fi wannan kaskanci a kasar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullun
Jihar Imo - Masu kallo da dama sun girgiza yayin da wata jami'ar yar sanda ta rera wakar taken kasar cike da kura-kurai a wani taron manyan jami'an yan sanda a Owerri, jihar Imo.

Kara karanta wannan
Babu inda zan tafi, Atiku ya magantu kan mataki na gaba bayan hukuncin kotun koli
Bidiyon jami'ar yar sandar tana tsallake wasu baitoci wajen rera taken kasar ya yadu a dandalin soshiyal midiya.

Asali: Facebook
Wani mai amfani da dandalin X @IamNobody_fr, ne ya wallafa bidiyon a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli bidiyon a kasa:
Yan Najeriya sun yi martani kan bidiyon yar sanda tana rera taken kasa
Taron wanda aka watsa kai tsaye a gidajan talbijin ya haddasa cece-kuce a tsakanin yan Najeriya.
@TinyAlonge ta yi martani:
"Cikakken bayanin halin da rundunar npf ke ciki."
k blurnt, @kendrick_fisay, ya ce:
"Za mu iya zuwa kasa da haka?"
@adu_faye ya ce:
"Yaya aka yi ta kammala makarantar yan sanda."
@stephcrown06 ta yi martani:
"Gaba dayanku da kuke yi wa matar nan dariya ba za ku iya rera kamar haka ba, lmao."
@NostalgicVibeNG ta ce:
"Abun da ke faruwa kenan idan mutane suka kai manyan mukaman yan sanda saboda sanayya ba wai don cancanta ba."

Kara karanta wannan
Kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba, tsohon rasiti ya nuna yadda aka biya N340 kudin makaranta
@anyidon247 ta yi martani:
"Wannan ya bayyana gaba daya rundunar sojin Najeriya."
Amarya ta yi jugum a wajen bikinta
A wani labarin, bidiyon shagalin bikin wata amarya yar Najeriya da ta tsaya jugum tana kallo yayin da angonta ke taka rawa cike da farin ciki ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.
Wani dan TikTok da ya wallafa bidiyon ya yi mamakin yadda amaryar ta kasance mai kunya tare da yin barkwanci game da rawar da angon ya taka.
Asali: Legit.ng