Ni Zan Rera Wakar Taken Kasa Idan Aka Sauyawa Najeriya Suna, Inji Naira Marley
- Shahararren mawaki Naira Marley ya bayyana aniyarsa ta rera sabuwar wakan take ga sabuwar kasa
- Ana ta cece-kuce bayan tura kudurin sauyawa Najeriya suna zuwa Hadaddiyar Jamhuriyar Afrika (UAR)
- A nasa gudunmawa, Naira Marley ya ce zai dauki babban aikin rera wa kasa take idan magana ta tabbata
Shahararren mawaki, Naira Marley ya bayyana cewa zai yi zaman jira don rera sabuwar wakar taken kasa bayan yanke shawarar sauya sunan Najeriya zuwa Hadaddiyyar Jamhuriyar Afirka (UAR).
A cewar rahotanni, Adeleye Jokotoye, kwararre kan haraji, ya gabatar da shawarar ga kwamitin a taron sauraron kararrakin yankin Kudu maso Yamma da ke Legas a ranar Laraba, 2 ga Yuni, 2021, jaridar Pulse ta ruwaito.
Yayin da yake gabatar da wannan shawara, ya ce sunan Najeriya turawan mulkin mallaka ne suka tilastawa kasar kuma ya kamata a canza shi.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Nada Sabon Shugaban Riko
A nashi bangaren na gudunmawa, Naira Marley ya bayyana a shafinsa na Twitter don bayar da gudunmawarsa kyauta ga sabuwar kasar, UAR.
A cewarsa, ya yarda ya dauki matsayin Pa Benedict Odise wanda ya rera wakar taken Najeriya ta biyu a shekarar 1978.
Ya rubuta a Twitter: "Omo Ni ne zan rera sabuwar wakar taken UAR."
KU KARANTA: Babu Hadi: Lai Mohammed Ya Caccaki Masu Kwatanta Sheikh Gumi da Nnamdi Kanu
A wani labarin, Jaridar Pulse ta rahoto cewa kwamitin da ke sauraron maganar yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul ya karbi kudirin sauya sunan kasar nan.
Wani masani a kan sha'anin haraji, Adeleye Jokotoye, ya gabatar da kudiri a gaban wannan kwamiti da ke zama a Legas, a ranar 2 ga watan Yuni, 2021.
Kamar yadda jaridar Independent ta rahoto a jiya, abin da Adeleye Jokotoye yake so shi ne, a canza wa Najeriya suna zuwa kasar United African Republic.
Asali: Legit.ng