Kungiyar NLC Ta yi Fada da Ministan Tinubu, Sun Ki Yarda Ayi Zama da Shi a Taro
- Kwamred Joe Ajaero ya nesanta kungiyarsa ta NLC da Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong
- Shugaban NLC na kasar ya fadi abin da ya jawo sabanin ‘yan kwadago da Ministan yayin da ake neman mafita
- Ajaero ya ce an sabawa alkawarin da aka yi da Ministan wajen kawo karshen rigimar da ake yi a kungiyar NURTWA
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya yi shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Kungiyar NLC ta ‘yan kwadago ta yi barazanar gujewa taronta na yau da gwamnatin tarayya a kan batun yajin-aikinsu.
This Day ta ce shugabannin ma’aikatan Najeriyan sun ce ba za su zauna a kujera daya da Ministan kwadago, Hon. Simon Lalong ba.
Da yake magana da manema labarai jiya a Abuja, shugaban NLC na kasa, Kwamred Joe Ajaero ya ce an gayyace su taro a Aso Rock.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya ta kira 'Yan NLC
Joe Ajaero yake cewa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya kira su domin duba rahoton inda aka kwana wajen dabbaka alkawuran da aka yi.
Gwamnatin tarayya ta cin ma yarjejeniya da ‘yan kwadago bayan cire tallafin fetur.
Ajaero ya fadawa manema labarai cewa dalilin zaman na yau shi ne su duba su gani ko gwamnati ta cika alkawuran da ta daukan masu.
NLC ta yi bayanin abin da ya sa ba za ta shiga taron da Simon Lalong zai halarta ba.
Ajaero: Rigimar NLC da Simon Lalong
"Idan za ayi taron, dole ya zama babu Ministan kwadago da samar da ayyuka, ba za mu shiga taron da Ministan kwadago zai zauna ba.
Idan za ku tuna matsayarmu da mu ka dauka da kungiyar NURTW ita ce duka bangarorin rikicin su bar harabar saboda zaman lafiya.
Amma har yanzu ba ayi hakan ba. Saboda haka taron da za mu yi da gwamnatin tarayya, Ministan kwadago ba zai shiga ciki ba."
Baya ga haka, NLC ta dauki alwashin cigaba da zanga-zangarta a birnin Owerri na jihar Imo a dalilin sabaninta da Gwamnatin jihar.
IPOB ta yi galaba a kan Gwamnati
Ana da labari Nnamdi Kanu zai tashi da N8bn daga hannun Gwamnatin Tarayya tun da IPOB ta yi galaba a Kotu a kan ta'addantar da kungiyar.
Kotun da ke zama a Enugu ta share takunkumin da aka kakabawa ‘Yan kungiyar IPOB saboda haka aka ce daure Nnamdi Kanu ya saba doka.
Asali: Legit.ng