Tinubu Na Kokari: Jamus Ta Yi Wa Najeriya Shirgegen Albishir Daya Tak da Zai Sauya Akalar Kasar
- Shugaba Tinubu da sauran kasashen Afirka ta Yamma za su samu bagas yayin da Gwamnatin Jamus ta yi alkwarin samar musu da wuta
- Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya yi wannan alkawari ne yayin wata ziyara da ya kawo Afirka inda zai kwashe kwanaki biyu a Najeriya
- Scholz ya dauki alwaura da dama ga kasashen Afirka ta Yamma wurin kawo dauki a yawan juyin mulki da ake yi da rashin tsaro da kuma lantarki
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Kasar Jamus ta yi Najeriya alkawarin samar musu da wutar lantarki ingantacciya kuma mai rahusa.
Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz shi ya yi wannan alkawari inda ya ce za su samar da wutar ce har da sauran kasashen Afirka ta Yamma.
Wane alkwari Scholz ya yi ga Tinubu, ECOWAS?
Scholz ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai yayin wani taro da kungiyar ECOWAS a jiya Lahadi 29 ga watan Oktoba, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya ce Jamus na hadaka da kungiyar kasashen ECOWAS musamman ta bangaren yaki da juyin mulki da rashin tsaro da sauransu.
Har ila yau, Jamus ta sha alwashin taimakon kasashen da wutar lantarki mai rahusa da makudan kudade na tallafi don rage radadi na fatara, Trust Radio ta tattaro.
Yaushe Scholz ya kawo ziyara ga Tinubu?
A jiya Lahadin ce 29 ga watan Oktoba, Shugaba Tinubu ya karbi bakwancin Shugaban gwamnatin Jamus, Scholz a fadarshi da ke Abuja.
Scholz ya samu isa fadar ne da misalin karfe 3:40 wanda shi ne karon farko da ya kawo ziyara kasar tun bayan samun shugabancin a watan Disambar 2021.
Har ila yau, ya kawo ziyara ce ta kwanaki biyu inda su ka tattauna batutuwa da dama da ke damun kasar da ma Afirka gaba daya.
Shugaba Tinubu ya yi masa alkawarin shawo kan dukkan matsalar Najeriya da kuma abubuwan da ke batawa kasar suna a idon duniya.
Ana zargin Tinubu da fifita 'yan APC a mukamai
A wani labarin, an zargi Shugaba Tinubu da nuna wariya wurin nada mambobin jam'iyyar APC kwamishinonin zabe.
Wani dan jarida mai bincike a Najeriya , Fisayo Soyombo shi ya yi wannan zargi bayan shugaban ya nada su a makon da ya gabata a shafin Twitter a jiya.
Asali: Legit.ng