Da Dumi-Dumi: Jigon Jam’iyyar PDP a Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Jam’iyyar Ta Shiga Dimuwa
- Shugabar mata ta jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Farfesa Stella Effan-Attoe ta rasu a yau Lahadi 29 ga watan Oktoba
- Farfesa Stella ta kasance ‘yar asalin jihar Kuros Riba kuma wanda ta ba da gudunmawa sosai a ci gaban mutane da Najeriya
- Jam’iyyar PDP, ta bakin sakatarenta na kasa, Debo Ologunagba shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Lahadi 29 ga watan Oktoba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Jam’iyyar PDP na cikin jimami bayan mutuwar shugabar mata ta jam’iyyar, Farfesa Stella Effan-Attoe.
Jam’iyyar ta ce wannan rashi ba iya jam’iyyar PDP kawai ba ne, har ma da sauran ‘yan Najeriya baki daya, cewar Vanguard.
Meye PDP ke cewa kan rasuwar shugabar matan?
Sakataren yada labarai na PDP a matakin kasa, Debo Ologunagba shi ya bayyana rasuwar a cikin wata sanarwa a yau Lahadi 29 ga watan Oktoba a Abuja, Legit ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce PDP da ma sauran ‘yan Najeriya sun yi babbar rashi na Farfesan da ma sauran dalibai da kuma jihar Kuros Riba.
Martanin Atiku kan mutuwar shugabar PDP
Jam’iyyar ta kwatanta Stella a matsayin mace mai kamar maza wurin kishi da kuma kawo ci gaba a harkokin siyasa.
Wane gudunmawa shugabar matan PDP ta bayar?
Sanarwar ta ce:
“Mu na cikin jimami, jam’iyyarmu da ma kasa baki daya mun yi babbar rashin Farfesa Stella, wannan mutuwa babban gibi ce ba kawai ga PDP ba har ma jami’o’i da kuma jama’ar Kuros Riba.
Isra’ila da Falasdinu: Kungiyar Shi’a Ta Tura Gargadi Mai Kama Hankali Ga Tinubu Kan Ta’addancin Isra’ila
“Farfesa Stella ta kasance kwararriya wanda ta ba da gudunmawa a bangarori da dama, ba ta da girman kai ga ta da son mutane da tausayi.”
Sanarwar ta kara da cewa Stella ta taba rayuwar mutane da dama wurin ba da gudunmawa a ci gaban rayuwarsu da kuma kasa baki daya.
Wazirin Fika ya riga mu gidan gaskiya a jihar Kaduna
A wani labarin, Allah ya karbi rayuwar Wazirin Fika, Alhaji Adamu Fika bayan fama da doguwar jinya.
Fika ya rasu ne yayin da ya ke cikin jirgi bayan dauko shi daga kasar Ingila zuwa Najeriya.
Marigayin wanda tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ne ya rike mukamai da dama wanda ya ba da gudunmawa sosai a ci gaban kasar Najeriya.
Asali: Legit.ng