Mai wankin mota ya yi hadari motar Kwastoma kirar Benz yayin zuwa sayan sabulu

Mai wankin mota ya yi hadari motar Kwastoma kirar Benz yayin zuwa sayan sabulu

  • Wani mai sana'ar Car Wash ya kira ruwa bayan hawa motar kwastoma ba tare da izininsa ba a jihar Edo
  • A bidiyon da aka daura a Instagram, matashin ya hau motar kirar Marsandi domin sayan sabulu
  • Mutane a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu

Wani matashin mai sana'ar wankin mota ya kirawa kansa ruwa a jihar Edo inda ya ragargaza motar kwatoma kirar Mercedez Benz yayin zuwa sayan sabulun wanki.

@instablog9ja ta daura bidiyon motar a shafinta na Instagram.

Mai wankin mota ya yi hadari motar Kwastoma kirar Benz yayin zuwa sayan sabulu
Mai wankin mota ya yi hadari motar Kwastoma kirar Benz yayin zuwa sayan sabulu Hoto: @instablog
Asali: Instagram

Wanda ya nadi bidiyon ya bayyana cewa wani mai wankin mota ne ya buge motar yayinda ya tafi sayan sabulu.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 10 da aure, ya gwabje matarsa mai tsohon ciki saboda abinci, ta sheka barzahu

Matashin ya shiga bango da motar kuma ta ragargaje fiye da yadda ake tsammani.

Yace wannan abu ya faru ne a jihar Edo.

An kama Idris mai wankin mota a hanyarsa ta zuwa ya siyar da galleliyar motar da aka kawo wanki

A bara, Wani mai sana'ar wankin mota, Idris Ayotunde, ya shiga hannun jami'an rundunar'yan sanda bayan ya gudu da dankareriyar motar kwastomansa da ya kawo wanki, kamar yadda Punch ta rawaito.

Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Ogun ne suka kama Ayotunde bayan ya gudu da motar da aka bashi wanki a jihar Legas.

Ayotunde ya gudu da galleliyar motar zuwa jihar Ogun.

Matashin ya fara sana'ar wankin mota a tashar mota ta Jimoh da ke Shaha, Akowonjo, a jihar Legas bayan ya kammala karatunsa na HND.

Asali: Legit.ng

Online view pixel