Ya Kamata CBN Ta Sa a Daina Amfani Sabbin Takardun Naira da Buhari Ya Kawo, Malami Ya Fadi Dalilai

Ya Kamata CBN Ta Sa a Daina Amfani Sabbin Takardun Naira da Buhari Ya Kawo, Malami Ya Fadi Dalilai

  • Primate Elijah Ayodele ya yi kira da a janye soke amfani da sabbin takardun Naira na Najeriya, inda ya bayyana su a matsayin makirin shiri
  • Malamin ya bukaci gwamnan CBN, Yemi Cardoso, da ya amince da ci gaba da kasha tsofaffin takardun kudi, yana mai cewa sabon tsarin na da alaka da munanan manufofi
  • Bugu da kari, Primate Ayodele ya yi hasashen cewa Cardoso zai fuskanci kalubale da 'yan siyasa da kuma bankuna a lokacinsa

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Primate Elijah Ayodele ya shawarci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso, da ya janye dokar kawo sabbin takardun Naira da gwamnatin Buhari ta kawo.

Shugaban cocin na INRI ya ba da wannan shawarar ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Malamin Addini Ya Hango Gagarumin Matsala a Jihar Ondo, Ya Ce Gwamna Akerodlu Na Bukatar Addu'a

An nemi a soke amfani da sabbin Naira
Fasto ya nemi a hana amfani da sabbin Naira | Hoto: @DrYemiCardoso, @Nwaadaz, @primate_ayodele
Asali: Twitter

Babu alheri a sauya Naira, inji Primate

Da yake magana game da dalilin da ya sa ya nemi a janye sabbin takardun Naira, Primate Ayodele ya ce babu alheri a tattare da kudaden, kuma an yi su da mugun nufin dagula tattalin arzikin Najeriya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar malamin, kara buga sabbin takardun kudin zai jefa Najeriya cikin babbar asara, wacce za a iya kaucewa ta hanyar janye su kowa ya huta.

Primate Ayodele ya ce tsohon zubi da yanayin tsoffin kudin ya fi dacewa da Najeriya kuma ya kamata ya zama karbabben kudi daya tilo a kasar, rahoton Daily Post.

Halin da Cardoso zai shiga, inji malamin coci

A bangare guda, Primate Ayodele ya kuma fitar da wani hasashe game da wa’adin sabon gwamnan CBN da aka nada, Cardoso.

Ya ce gwamnan na CBN zai tabuka abin kirki amma zai samu matsala da ‘yan siyasa da kuma bankuna, inda ya gargade shi kan wasu tsare-tsare da za su shafi nasararsa.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari Ya Yi Ya Jawo darajar Naira ta ke Karyewa a Yau – Sanatan PDP

Ya kuma bas hi shawarin amfani da kudaden zamani wajen tabbatar da nasarar farfadowar tattalin arzikin kasar nan.

Sarkafe-sarkafen tsaro da ke jikin Naira

A wani labarin, Nigerian Security Printing and Minting Plc, fitaccen kamfanin buga takardu a Najeriya ya yi karin haske game da surkullen tsaron da ke cikin sabbin kudaden Naira da ya buga kwanan nan.

Ya bayyana cewa, wasu daga abubuwan da ‘yan Najeriya ke kokawa a kai game sabbin kudin ba komai bane face wata dabara ta ba kudaden kasar kariyar tsaro.

Wannan batu na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan kasar ke ci gaba da bayyana damuwa game da yadda sabon sauyin Naira ya zo da abubuwan da ba a yi tsammani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.