Tsohon Minista Solomon Dalung Ya Bayyana Mafiya 1 Kan Rikice-Rikicen Jihar Plateau

Tsohon Minista Solomon Dalung Ya Bayyana Mafiya 1 Kan Rikice-Rikicen Jihar Plateau

  • Rikicin ƙabilanci ya kashe ɗaruruwan mutane a shekarun baya-bayan nan a yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya mai bambancin ƙabila da addini
  • A cewar wani rahoto na baya-bayan nan daga cibiyar ACLED, a jihar Plateau mutane sama da 2,200 aka kashe tun daga shekarar 2005
  • Da yake magana a wata hira ta musamman da Legit.ng, Solomon Dalung, tsohon minista kuma ɗan asalin jihar Filato, ya tattauna kan ‘maganin’ matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jos, jihar Plateau - Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya ce adalci shi ne kaɗai mafita ga abin takaicin da ke aukuwa a jihar Plateau.

A cewar Dalung, "idan babu adalci, zaman lafiya baƙo ne."

Solomon Dalung ya yi magana kan rikicin Plateau
Tsohon minista Dalung ya yi magana kan rikicin Plateau Hoto: Barrister Solomon Dalung, The Time is Now, Haggai Gankis
Asali: Facebook

Dole ne gwamna Mutfwang ya yi adalci ga kowa

Dalung, wanda ya fito daga jihar Plateau, ya riƙe muƙamin ministan a tsakanin 2015 zuwa 2019, a lokacin wa'adin farko na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Bayyana Kananan Hukumomin Jihar Borno da Ke Karkashin Ikon Boko Haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa gwamnatocin Plateau da suka shuɗe sun yi ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin jihar da ke laƙume rayuka ciki har da na yara da mata, tashin hankalin ya ƙaru a lokacin da gwamna Caleb Mutfwang ya hau mulki a watan Mayu.

Da yake magana kan rikicin Plateau, a yayin wata tattaunawa da Legit.ng, Dalung ya bayyana cewa:

“Maganin rikicin Plateau ɗaya tilo shine adalci, duk sauran ƙoƙarin da gwamnatocin baya suka yi, ba tare da aniyar tabbatar da adalci ba surutu ne kawai. Idan babu adalci, zaman lafiya baƙo ne."

"Domin haka, idan har gwamna Mutfwang ya ƙudiri aniyar shawo kan matsalar Plateau, dole ne ya tsaya tsayin daka, ya zama mai azama, kuma ya yi adalci.”

Ya cigaba da cewa:

"Rikicin da ake fama da shi a Plateau ya kasance tun 2001. An kashe mutane da dama. Muna da yaran da a yanzu ba su zuwa makaranta kuma sun zama marayu, muna da ɗaya daga cikin masu yawan zawarawa, an lalata wuraren kiwon lafiya da kasuwanni. Domin haka idan har ya zama tilas a kawo ƙarshen wannan lamari, dole ne mu yi adalci kan lamarin.”

Kara karanta wannan

Ke Duniya: Yadda Matashin Yaro Ya Halaka Babbar Mace Yar Shekara 58 a Jihar Arewa

A ƙarshe Dalung ya ce idan har gwamnatin Plateau ta yanzu ta ƙudiri aniyar kawo ƙarshen rikicin, to dole ne ta rungumi adalci, ta tafi tare da dukkanin ƙabilun jihar, tare da yi wa kowa adalci.

"Duk wani abu baya ga waɗannan surutu ne kawai wanda ke da buri na siyasa, amma ba zai iya samar da wani sakamako mai ɗorewa ba." A cewarsa.

Buhari Na Rayuwar Nadama, Dalung

A wani labarin kuma, tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya koma rayuwar nadama bayan ya bar mulki.

Dalung ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasar yana nadama ne kan yadda muƙarrabansa suka ɓata masa suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng