Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Hakimi Da Mutum 5 a Zamfara

Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Hakimi Da Mutum 5 a Zamfara

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kutsa garin Ruwan Rana da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara a daren Asabar
  • Yan bindigan sun bi gida-gida sun sace mutane biyar cikinsu har da hakimin garin, Alhaji Magaji Makau, sannan sun halaka wani mutum daya
  • Muhammad Musa, wani mazaunin garin na Ruwan Rana ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da bayanin yadda harin ya faru

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Zamfara - Yan bindiga sun sace hakimin garin Ruwan Rana a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara, Magaji Makau da wasu mutane biyar a safiyar ranar Asabar.

Hakazalika, an kuma kashe wani mutum yayin harin.

Yan bindiga sun tafi gida sun sace hakimi a Zamfara
Yan bindiga sun tafi da hakimi da wasu mutane 5 daji a Zamfara. Hoto: Hedkwatar Tsaro ta Najeriya
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Daga Yin Barazanar Tsige Gwamna, Majalisar Dokoki ta Kama da Wuta Cikin Dare a Ribas

Wani mazaunin garin, Muhammad Musa, ya fada wa The Punch cewa, yan bindigan biyu da suka taho kan babur sun shigo garin Rana da asubahin ranar Asabar.

Mazaunin gari ya magantu kan sace hakimin Zamfara

Musa ya ce yan bindigan, wadanda suka iso garin misalin karfe 3 sun fara harbe-harbe sannan daga bisani suka fara zuwa gida-gida suka sace hakimi da wasu fitattun mutane biyar, Vanguard ta rahoto.

Ya kuma yi bayanin cewa sun kashe wani mutum daya da ya ki yarda a tafi da shi.

Ya ce:

"Mun ji karar harbi misalin karfe 3 na safe kuma koya ya boye saboda mun san yan bindigan sun taho sace mutane ne.
"Sun rika zuwa gida-gida kuma suka sace mutane biyar ciki har da hakiminmu, sun harbe mutum daya, daga baya suka koma daji.
"Ban san wadanda suka sace ba sai da gari ya waye na fito na ji cewa hakimi, Alhaji Makau na cikin wadanda aka sace."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban karamar hukuma a Benue bayan sace shi na kwanaki

Dan Majalisa ya nuna damuwarsa kan lamarin

Wani dan majalisar jihar mai wakiltar yankin, Hon. Hamisu Faru, ya nuna barin ransa kan lamarin yana mai bada tabbacin za a ceto wadanda aka sace.

Ya ce:

"Jami'an tsaro na kokarin ceto hakimi da sauran mutanen biyar."

Ba a samu ji ta bakin kakakin yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ba, don ba a same shi ba lokacin hada wannan rahoton.

Dan Majalisa: Abin Da Yan Bindigan Zamfara Ke Bukata

A bangare guda, Kabiru Ahmadu, dan majalisar tarayya mai wakiltar Gusau/Tsafe a Zamfara ya fadi abin da yan bindiga ke bukata daga gwamnati.

A cewarsa yan bindigan sun tsananta hare-hare ne don suna neman gwamnati ta nemi yin sulhu da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164