Bidiyon Yanayin Kallon Da Amarya Ke Yi Wa Angonta Yayin da Yake Tikar Rawa Ya Girgiza Intanet

Bidiyon Yanayin Kallon Da Amarya Ke Yi Wa Angonta Yayin da Yake Tikar Rawa Ya Girgiza Intanet

  • Jama'a sun yi cece-kuce kan yanayin wata amarya Bahaushiya yayin da suke taka rawa da angonta
  • Yayin da angonta da ke cike da farin ciki ya baje kolin rawarsa, amaryar ta tsaya jugum tana kallonsa cike da kunya
  • Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun nuna sha'awarsu ga yadda angon ya taka rawa, yayin da wasu suka yi barkwanci kan yanayin amaryar

Bidiyon shagalin bikin wata amarya yar Najeriya da ta tsaya jugum tana kallo yayin da angonta ke taka rawa cike da farin ciki ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Wani dan TikTok da ya wallafa bidiyon ya yi mamakin yadda amaryar ta kasance mai kunya tare da yin barkwanci game da rawar da angon ya taka.

Amarya ta zurawa ango idanu yayin da yake tikar rawa
Bidiyon Yanayin Kallon Da Amarya Ke Yi Wa Angonta Yayin da Yake Tikar Rawa Ya Girgiza Intanet Hoto: @donjerry000
Asali: TikTok

Sai kace dan nanaye, angon ya dunga taka rawa cikin salo a bidiyon yayin da ya mahalarta bikin suka dungi kallon yadda yake rawa cikin farin ciki.

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Yi Ikirarin Soya Kaza Da Ruwa, Ya Saki Bidiyon Tsarin Da Ya bi

Amaryarsa ta tsaya a gefe guda sannan ta zuba ido tana kallonsa. Alamu sun nuna matashiyar na jin kunya, Yayin angon wanda yake Bahaushe ya sace zukatan masu kallo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya samu mutane miliyan 1.8 da suka kalla yayin da suka dungi jinjinawa rawar da angon ya taka. Wasu sun cika da mamakin dalilin da yasa amaryar ta yi abun da ta yi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon aure

Samiratu ta ce:

"Shakka babu zan tattauna wannan da mijina saboda ba na so irin haka ta faru da ni."

Bibi_couture_kids ta ce:

"Ba a haifi matar ta yi rawa babu kamun kai ba. A arewa take fa."

Mai gadon zinari ta ce:

"Ku bar shi ya yi rawa fa irin rawar murnan nan a karshe na samu mata..ya fita daga layin gauro.

Kara karanta wannan

“Ke Attajira Ce”: Jama’a Sun Yi Martani Yayin da Budurwa Ta Fasa Asusunta, Ta Baje Kolin Kudin

Ayevbosa Ann ta ce:

"Na zata amaryar na cikin yan a ci biki ne, me yasa take kallonsa haka???mtweeee."

zeejay ta ce:

"Tana yi kamar tana jin kunya har sai an kai dayan dakin tukuna."

Joycee ta ce:

"Mazan Hausawa na da kyau sosai. A matsayina na bayarabiya, zan so na auri bahaushe mai ilimi."

Akuya ta makale a cikin buta

A wani labari na daban, an yi nasarar ceto wata akuya da kanta ya makale a cikin wani buta bayan makwabta sun taru a wajen.

A cikin wani bidiyo mai ban dariya da ya yadu a soshiyal midiya, alamu sun nuna akuyar tana neman abun sakawa a baki a cikin butan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng