Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Gwanjar da Barikokin ’Yan Sanda, Ta Bayyana Dalilai
- Yayin da barikokin ‘yan sanda a Najeriya ke cikn mawuyacin hali, majalisa ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta jinginar da su
- Majalisar ta yi wannan a kiran ne a ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba a Abuja yayin zaman majalisar da aka yi
- Mamba mai wakiltar wata mazaba a jihar Edo, Murphy Omoruyi shi ya yi wannan kira yayin gabatar da wani kuduri a majalisar
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta gwanjar da barikin ‘yan sanda a kasar saboda lalacewarsu.
Wannan na zuwa ne bayan kuduri da mamban majalisar, Murphy Omoruyi daga jihar Edo ya gabatar a dakin majalisar a Abuja a ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba.
Wane bukata majalisar ta gabatar ga Gwamnatin Tarayya?
Majalisar ta bukaci ma’aikatar cikin gida da ta hada karfi da hukumar BPE don sanin farashin barikokin a kasar baki daya, Daily Trust ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce wannan kuduri zai taimaka wurin sake gina barikokin da su ka lalace saboda rashin kulawa na gwamnati.
Yayin gabatar da kudurin, Omoruyi ya tunatar da majalisar cewa ta tabbatar da kudirin gyara a aikin dan sanda a 2020 wanda tsohon shugaban kasa, Buhari ya sanya wa hannu.
Wane shawara majalisar ta bai wa Gwamnatin Tarayya?
Omoruyi ya ce matsalar samar da isassun wurin zama da ingantaccen tsari na ‘yan sandan ya na kara kamari da ya ke son fin karfin hukumomi.
Ya ce:
“Misali a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022, Gwamnatin Tarayya ta kashe naira biliyan biyar kawai don gyaran barikokin ‘yan sanda a kasar.
“Duk wannan kokari, barikokin sun ci gaba da rugurgujewa saboda rashin samun kulawa da sauran gyare-gyare.”
Ya kara da cewa yin amfani da wannan tsari na ajiye barikokin a matsayin matsugunin ‘yan sandan tsohon ya yi ne, Daily Post ta tattaro.
Majalisar wakilai ta koka kan yadda mabarata ke damunsu
A wani labarin, majalisar wakilai ta Tarayya ta nuna damuwa kan yadda mabarata ke cika musu ofisoshi tare da rokon su kudade.
Majalisar ta bayyana cewa direbobin tasi na ‘Uber’ da ‘Bolt’ su ma sun addabesu inda har ta kai su na hanasu shige da fice a majalisar.
Asali: Legit.ng