Kano: Abba Kabir Ya Ware Biliyan 6 Don Saka Wa 'Yan Fansho, Ya Soki Ganduje
- Gwamnatin jihar Kano ta ware naira biliyan shida don biyan basukan ma’aikata da su ka rasa ransu yayin aikin gwamnati
- Har ila yau, gwamnatin za ta biya basukan ‘yan fansho da aka rike musu kudade bayan sun gama bautawa gwamnatin jihar
- Gwamna Abba Kabir shi ya bayyana haka inda ya ce gwamnatin da ta shude ta azabtar da ma’aikatan jihar
Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sanar da fara biyan makudan kudade don ma’aikatan da su ka mutu da ‘yan fansho.
Gwamnan ya ce gwamnatin ta ware naira biliyan shida ga ma’aikatan da su ka mutu da ‘yan fansho fiye da dubu biyar a jihar.
Meye Abba Kabir ya ce kan ma’aikata?
Abba Kabir ya nuna damuwarshi kan tarun kudaden da gwamnatin da ta shude wanda ya kai fiye da naira biliyan 40 ta bari, Tribune ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Zuwa wani mako, za su karbi kudadensu da su ke bin gwamnati da yardarn Allah, akalla kudaden da mu ka lissafa sun kai naira biliyan shida.
“Ina son tabbatar mu ku da cewa, mu na da kudaden a kasa domin ba bashi mu ka ciyo ba.”
Wane alwashi Gwamna Abba Kabir ya yi?
Abba Gida Gida ya sha alwashin biyan dukkan basukan inda ya tabbatar cewa hakan ya samu sahalewar majalisar zartarwa ce a ganawarsu ta ranar Laraba 25 ga watan Oktoba.
Ya nuna damuwa da tausayawa ga ma’aikata wadanda su ka bautawa jihar amma kuma aka tauye mu su hakkokinsu a gwamnatin da ta shude.
Ya kara da cewa:
“Ina yawan tunawa da matsalar biyan basuka na fanshon ma’aikata, kuma ina yawan ganawa da babban akanta janar na jihar da sauran ma su ruwa da tsaki don samun mafita.”
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin kyautatawa ma’aikata da su ke aiki da kuma wadanda su ka yi ritaya a jihar, Daily Post ta tattaro.
Abba Kabir ya dauki nauyin dalibai zuwa ketare
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya dauki nauyin dalibai 1001 zuwa kasashen Indiya da Uganda don karo karatu.
A ranar Juma’a ce 20 ga watan Oktoba kason farko na daliban guda 550 su ka tashi zuwa kasar Indiya.
Asali: Legit.ng