Albishir Ga ’Yan Crypto, Abu 1 Ya Sa Bitcoin Ya Tashi a Najeriya, Ajantina da Turkiyya
- Farashin kudin intanet na Bitcoin ya tashi a Najeriya, Turkiyya, da Ajantina a ranar Juma'a, 27 ga Oktoba, 2023
- Wannan ya biyo bayan hauhawar farashin kayayyaki ne a kasashen uku, wadanda kuma ke fuskantar faduwar darajar kudi
- Rahotanni sun ce Najeriya na ta sassauta matsayarta kan kasuwancin crypto yayin da akasarin ‘yan kasar ke neman hanyar fakewa karywar darajar kudin kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Farashin kudin Bitcoin na ci gaba da azalzalar tsada a wasu kasashen duniya uku da ke fuskantar karyewar darajar kudadensu.
Wadannan kasashe sune Najeriya, Ajantina da Turkiya, kamar yadda rahoton da muka tattaro ya bayyana.
Ya zuwa safiyar Juma'a, 27 ga Oktoba, 2023, Bitcoin ya yi tashin gwauron zabo a Najeriya, Turkiyya, da Argentina yayin da 'yan kasar suka koma siyan kudaden intanet don tsira da darajar kadarorinsu.
Yadda farashin yake a kasashen uku
An yi harkallar Bitcoin a kan kudi Naira miliyan 28.4 a Najeriya, peso miliyan 12.4 a Ajantina da kuma Lira 979,000 a kasar Turkiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An alaknta da tashin farashin wannan kudi na intanet da yadda darajar kudaden kasashen guda uku.
Asusun ba da lamuni na duniya ya ce Ajantina na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki kusan da ninki uku, inda kudin kasar ke matsayi na hudu a jerin kudaden da aka fi samun hauhawar farashin kayayyaki a shekara.
Kudin Turkiyya da Naira na kan matsayi na 6 da 15 bi da bi, inda hauhawar farashin kaya ya karu da 25% da 52% bi da bi a cikin shekarar da ta gabata a wadannan kasashe.
A bangare guda, wannan tashi ya jawo mai kamfanin Binance ya samu faduwar akalla $12bn a lokaci guda.
Hukuncin Kotun Koli: Ganduje Ya Bayyana Shekarar da Ya Kamata Atiku da Peter Obi Su Yi Takarar Shugaban Kasa
Matsayin Najeriya a duniyar crypto
Bincike ya nuna cewa, Najeriya ce kasa ta biyu a duniyar crypto, inda adadi mai tsoka na 'yan kasar, musamman matasa ke ta'ammuli da kudaden intanet.
A baya, gwamnatin Najeriya ta kirkiri kudi mai kama da na cypto; eNaira don taimakawa hada-hadar kudi a kasar.
Sai dai, har yanzu bai samu wata karbuwar da ake tsammanin ta samu ba tun farkon samuwarta a 2022.
An sha kudi a crypto
A baya, da yawan ‘yan crypto a Najeriya sun wayi gari da tarin biliyoyin daloli a asusunsu yayin da wata kafar crypto ta samu matsalar fasaha.
Bayan da Legit.ng ta yada labarin Chinedu MacGordon da ya wayi gari da tarin biliyoyi a asusun crypto dinsa, jama’a da yawa ne suka yi martani da labari mai kama da nasa a kafar Facebook.
Da yawan mutane sun bayyana cewa, sun ga tarin kudi a asusunsa na Coinbase, kuma sun yi kokarin cire kudin, amma hakan ya gagara.
Asali: Legit.ng