An Shiga Tashin Hankali Bayan ’Yan Bindiga Sun Fille Kan Babban Dan Sanda, Jami’an Sun Yi Martani
- Wani jami’in dan sanda ya gamu da tsautsayi bayan wasu tsagera sun fille kansa yayin wani farmaki da su ka kai a jihar Abia
- Dan sandan ya rasa ransa ne bayan ‘yan bindigan sun farma wurin binciken ababan kan hanyar Umuode zuwa Isiahia da ke jihar
- Sai dai kakakin rundunar ‘yan sanda, Maureen Chinaka ya musanta cewa an kashe dan sandan inda ya ce dan sa kai su ka fille wa kai
Jihar Abia – ‘Yan bindiga a jihar Abia sun guntule kan wani jami’in dan sanda a wurin binciken ababan hawa.
Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 26 ga watan Oktoba a kan hanyar Umuode zuwa Isiahia a karamar hukumar Osisioma Ngwa da ke jihar.
Yaushe ‘yan bindigan su ka fille kan dan sandan?
The Nation ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe hudu na yamma wanda ya yi sanadin rikicewar al’ummar yankin saboda tsoron me abin da zai biyo baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun tabbatar da cewa sauran jami’an ‘yan sandan sun tsere don neman tsira yayin ‘yan bindigan su ka fille kan dan sandan.
Majiyar ta tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun rufa ‘yan sandan da gudu inda su kuma su ka arce da makamansu don neman tsira da rayukansu.
Wane martani ‘yan sanda su ka yi kan ‘yan bindigan?
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sanda, Maureen Chinaka ya musanta cewa an kashe dan sandan inda ya ce maharan sun fille kan dan sa kai ne a yankin.
A watannin baya, wasu tsagera sun fille kan wani babban jami’in ‘yan sanda a kan hanyar East da ke karamar hukumar Aba ta Kudu da ke jihar Abia, cewar Vanguard.
Kudu maso Gabashin kasar na fama da hare-haren ‘yan bindiga wanda ya yi sanadin rayuka da dama da ake zargin ‘yan IPOB.
‘Yan sanda sun kama matar da ta watsawa mijinta man gyada
A wani labarin, rundunar ‘yan sanda a jihar Ribas ta cafke wata mata mai suna Hope da zargin watsawa mijinta tafasasshen man gyada a jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mijin da matar sun samu wata ‘yar hatsaniya ce tsakaninsu da ya yi sanadin faruwar hakan.
Asali: Legit.ng