"Allah Ne Ke Kare Mu": Yar Najeriya Ta Saki Bidiyon Kazantaccen Muhallin da Ake Samar da Man Ja

"Allah Ne Ke Kare Mu": Yar Najeriya Ta Saki Bidiyon Kazantaccen Muhallin da Ake Samar da Man Ja

  • Wata matashiya yar Najeriya ta bai mutane mamaki da bidiyon da ke nuna yadda take sarrafa man janta
  • Wasu mutane da suka ga bidiyon sun ce basu san haka ake yin man ja a wuri mai datti kamar wannan ba
  • Yankin ya yi kama da wurin tabo, amma wasu mutane sun ce ba wani abu bane, yayin da wasu suka nuna rashin jin dadi kan haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jama'a sun yi cece-kice kan bidiyon wata matashiya da ke nuna muhallin da take sarrafa man ja.

Bidiyon da aka wallafa a Twitter ya bai mutane mamaki saboda wurin na da datti sosai da tabo.

Matashiya ta nuna yadda ake yin man ja
Yar Najeriya Ta Saki Bidiyon Kazantaccen Muhallin Da Ake Samar Da Man Ja Hoto: Twitter/@postsubman.
Asali: UGC

An gano ta a cikin wani rami mai tabo yayin da man ja ke yawo a sama. Tana ta jujjuya abun da ya yi kama da ruwan datti da bokitinta. Daga bisani sai ta ajiye bokitin sannan ta ci gaba da jujjuyawa da hannu.

Kara karanta wannan

“Ka Kace a Kauye”: Yar Najeriya Ta Je Neman Gida a UK, Ta Ci Karo Da Unguwanni Masu Datti Da Kazanta a Bidiyo

Yanayin yadda muhallin ke dauke da tabo da rashin tsaftar wurin ya sa wasu mutane da suka kalli bidiyon cikin damuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu sun bayyana cewa basu san haka ake yin man ja.

Wasu masu amfani da soshiyal midiya sun yi karin haske cewa tsarin samar da irin wannan kaya abu ne na wani yanki a Najeriya kuma cewa ba abu ne na gama gari ba. Shafin @postsubman ne ya wallafa bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Yan Najeriya sun yi martani kan sarrafa man ja

@ownMyShame ta ce:

"A baya yadda ake sarrafa mai da soya garin kwaki yana hana mani bacci. Harabar gidanmu kan cika da mutane, hayaniya da tsuma daga wutan icce."

@GoldenTVUpdate1 ya tambaya:

"Idan kuma tana al'adarta fa? Baaba mutane sun yi amfani da jinin al'ada wajen soya miya sun ji babu dadi."

Kara karanta wannan

“Wannan Aure Akwai Matsala”: Rudani Yayin da Bidiyon Wani Ango Da Amarya Ya Jefa Mutane Cikin Damuwa

@Official_Hydar ya tambaya:

"Wayyo Allah, da fatan bata wanke wannan abun a cikin man jan?"

@HardinDude ta ce:

"Kuma mun dade muna yi wa abincin Indiya dariya."

@maji_san ta ce:

"Allah ne ke kare mu da dadewa."

Jirgin sama zai koma amfani da man ja

A wani labarin, jiga-jigai a bangaren harkar jiragen sama sun ce Najeriya ta kai matsayin da za ta fara neman abun da zai maye gurbin man jirgi.

A rahoton da aka fitar a Daily Trust, hakan ya zama dole ne ganin makudan kudin da ake kashewa wajen shigo da mai daga ketare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng