Jerin Jihohin Da Shinkafa, Wake, Burodi Da Gari Suka Fi Tsada Da Araha A Najeriya

Jerin Jihohin Da Shinkafa, Wake, Burodi Da Gari Suka Fi Tsada Da Araha A Najeriya

  • Hauhawan farashin kayan abinci a Najeriya ya jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali
  • Bugu da kari, wasu abincin da aka saba amfani da su yau da kullum suna kara tsada a kasuwannin kasar
  • Shinkafa, wake, garri, burodi, da wasu nau'in abinci da yawa duk sun kara kudi da kashi 20 cikin 100

Hukumar kididdiga ta Najeriya, NBS, ta bada bayanin yadda farashin kayan abinci suka tashi a watan Yuli a kasar.

A cikin rahoton da ta wallafa na wasu zababen kayan abinci a shafinta na yanar gizo, NBS ta ce manyan kayan abinci a kasar sun kara tsada.

Akwai nau'in abinci guda 25 a rahoton wadanda suka hada da wake, burodi, naman shanu, gari, albasa, man ja, tumatur, fulawa da doya.

Farashin Kayan Abinci na Yuli
Jihohin Da Shinkafa Wake, Burodi Da Gari Suka Fi Tsada Da Araha A Najeriya. Hoto: NBS
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Dabarar da Bankuna Suke Bi Domin Cin Riba Kan ‘Yan Najeriya Wajen Canjin Dala

Wake

A cewar rahoton na NBS, farashin da aka saba gani yau da kullum na 1kg na wake (fari, baki) a watan Yulin 2022 shine N547.38, hakan na nufin an samu karin 23.22% daga N444.21 a watan Yulin 2021.

Jihar ta wake ya fi tsada itace Ebonyi a watan Yulin 2022 inda ake sayar da da mudu N900.51, yayin da jihar da waken ya fi araha ita ce Borno, N317.73.

Tumatur

A bangaren tumatur, NBS ta ce an samu karin 2.09% daga N536.17 a watan Yunin 2022.

Galibi akan sayar da 1kg na tumatur kan N446.81 a watan Yulin 2022, an samu karin 7.71% daga N414.83 daga watan Yulin 2021.

Jihar da tumatur ta fi tsada itace Edo da ake sayar da 1kg kan N799.16, yayin da jihar da tumatur ya fi araha itace Taraba da ake sayarwa kan N159.14.

Naman Shanu (banda kashi)

Kara karanta wannan

Jerin Jihohi Masu Arhar Kalanzir da Gas Ɗin Girki Da Jihohi Masu Tsada a Najeriya

Jihar da naman shanu ya fi araha a watan Yuli ita ce Taraba inda ake sayar da 1kg kan N1,500, yayin da Edo ce jihar da naman ya fi tsada inda ake sayar da 1kg kan N2,710.43

Shinkafa

Alkalluman na NBS ya nuna cewa tsaka-tsakin farashin 1kg na shinkafa a watan Yulin 2022 shine N467.80, hakan na nuna an samu karin 13.55% daga (411.97) da ake sayarwa a watan Yulin 2021.

Yankin da shinkafa ya ci tsada shine Arewa maso Yamma inda ake sayar da 1kg kan N796.03 a watan Yuli, yankin da ke biye da shi kuma shine Kudu maso Yamma da ake sayarwa N519.64, inda kuma shinkafan ya ci araha shine Arewa maso Tsakiya, N401.72.

Burodi

Jihar Plateau ce inda burodi ya fi araha a watan Yulin 2022 kan (296.25) yayin da jihar Abia ne burodi ya fi tsada inda ake sayar da 500g kan (672.03).

Kara karanta wannan

An Gama Jiran Watanni, Muhammadu Buhari Ya Rattaba Hannu a Sababbin Dokoki 8

Jerin Kasashen 15 Afirka da Ke Fama da Hauhawar Farashin Abinci a 2022

A cewar wani rahoto daga jaridar Business Insider, lamarin hauhawar farashin kayayyaki a duniya ciki har da nan Najeriya da sauran kasashen Afirka, shi jawo tsadar rayuwa da al'umma ke ciki.

Yakin Rasha da Ukraine ne dalilin da kawo hauhawar farashin abinci, kasancewar kasashen biyu ne ke kan gaba wajen samar wadatacciyar alkama, sauran nau'ikan abinci da muhimman hatsi da ake amfani dasu yau da kullum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel