Gobara ta kone shaguna 70 a kasuwar zamani na Minna

Gobara ta kone shaguna 70 a kasuwar zamani na Minna

A kalla shaguna 70 ne suka kone tare da dukiyoyi na miliyoyin naira sakamakon wata gobara da ta afku a safiyar yau Juma'a a kasuwar zamani na Abdulkadir Kure da ke Minna a jihar Neja.

Daily Trust ta ruwaito cewa gobarar ta fara ne daga shagon wani mai sayar da shayi da ke kusa da layin shagunnan masu sayar da man ja misalin karfe 6 na safiyar yau.

Wasu shaidun ido sun ce man gyada da man ja da ke shagunan ne ya kara asassa gobarar har ta kai ga kone shaguna da yawa kafin jami'an kwana-kwana su iso wurin sun kashe gobarar.

Gobara ta kone shaguna 70 a kasuwar zamani na Minna
Gobara ta kone shaguna 70 a kasuwar zamani na Minna
Asali: Twitter

Daga bisani gobarar ta sake tasowa daga daya daga cikin shagunan da ke kulle misalin karfe 11 na safiya kuma ta kara bazuwa zuwa wasu shagunan.

DUBA WANNAN: An nadi faifan bidiyon wani malamin islamiyya yana lalata dalibarsa mai shekaru 5

Duk da cewa ba a gano takamamen abinda ya hadasa gobarar ba, wasu suna ganin akwai yiyuwar mai shayin ya kuna murhunsa ne ya tafi sallar asuba wadda hakan ya yi sanadiyar gobarar kafin ya dawo daga masallaci.

Shuagaban kungiyar 'yan kasuwan Kure, Alhaji Yusuf ya ce ya yi asarar galolin manja guda 400 wanda kowannensu kudinsa N10,000 wadda ke nuna ya yi asarar N40,000,000.

Ya ce abu ne mai wahala a kiyasta asarar da akayi a yanzu a tare da anyi cikaken bincike ba.

Wani dan kasuwa, Mallam Alhassan Husseini ya ce ya yi asarar kaya na kimanin Naira Miliyan 1 da tsabar kudi kimanin N300,000 sakamakon gobarar.

A yayin da ya kai ziyara kasuwar, Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar ya ce gobarar abin bakin ciki ne da tausayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164