“Magana Ta Gaskiya, Wike Na Da Laifi”: MURIC Ta Magantu Bayan Wike Ya Kira Minista Shaidani

“Magana Ta Gaskiya, Wike Na Da Laifi”: MURIC Ta Magantu Bayan Wike Ya Kira Minista Shaidani

  • Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a kwanan nan kan karban bakuncin jakadan Isra'ila a ofishinsa
  • A bidiyo mai tsawon mintuna 14 da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, Gumi ya bayyana Wike a matsayin shaidani
  • MURIC ta shiga cikin lamarin sannan ta ce Sheikh Gumi na da yancin bayyana abun da ke ransa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ta ba shi dama

FCT, Abuja - Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC, ta ce yawancin wadanda ke mayarwa Sheikh Ahmad Gumi martani suna yin hakan ne saboda raunin zuciya, ba wai don lura da zahirin gaskiya ba.

Koda dai Gumi ya sha caccaka daga bangarori da dama kan furucinsa, MURIC ta tashi tsaye don kare Shehin malamin.

Kara karanta wannan

ICPC: Jerin Mutum 8 da Su ka Rike Shugabancin Takawarar EFCC a Tsawon Shekara 23

MURIC ta goyi bayan Gumi a kan Wike
“Magana Ta Gaskiya, Wike Na Da Laifi”: MURIC Ta Magantu Bayan Wike Ya Kira Minista Shaidani Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, Muslim Rights Concern
Asali: Facebook

"Wike na da laifi": MURIC ta kare Gumi

MURIC ta ce ra'ayinta ya dogara ne akan abubuwan da Wike ya aikata, "saboda idan babu rami me ya kawo maganar rami".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya aikewa Legit Hausa a ranar Laraba, 25 ga watan Oktoban 2023.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"An dauki maganar Gumi a kaikaice sai kace Shaykh ya wayi gari ne daga bacci sannan ya fara magana. Dole akwai abun da ya ingiza shi. Me yasa bai caccaki wani ministan ba? Me yasa sai Wike kadai cikin dukka ministocin? Ya kamata a tantance furucin da Gumi ya yi a kan Wike a kan abubuwan da Wike ya aikata da kuma kalaman da aka furta idan muna son gaskiya.
"Magana ta gaskiya ita ce Wike yana da laifi. Ya dade yana ta babatu. Ya kuma nuna kin jinin Musulmi. A matsayin gwamnan jihar Ribas, Wike ya rushe wani masallaci a Port Harcourt duk da rokon da aka yi."

Kara karanta wannan

Nyesom Wike Ya Kinkimo Doka, Marasa Biyan Haraji Za Su Tafi Kurkuku a Abuja

MURIC ta kara da cewar:

"Gayyatan da Wike ya yi wa jakadan Isra'ila kasance mai tsananin gaske. Ya bar wa ministan harkokin waje wannan."

Igboho ya caccaki Gumi kan maganganunsa

A gefe guda, mun ji cewa ana ci gaba da caccakar Sheikh Ahmed Gumi saboda kalamansa kan Nyesom Wike da kuma gwamnatin Bola Tinubu.

Gumi ya zargin gwamnatin Tinubu da fifita Kiristoci da kuma kiran shugaban da ya tube Wike a mukaminsa tare da nada Musulmi, Tribune ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng