Yan Sanda Sun Kama Mutum 6 Kan Kisan Diyar Dan Majalisar Borno
- Rundunar yan sandan jihar Borno ta yi nasarar kama wasu mutum shida da ake zargi a kan kisan diyar dan majalisar jihar, Fatima Bukar
- Jami'an yan sanda sun yi amfani da lambar IMEL din wayar marigayiyar da aka nema aka rasa bayan kasheta wajen gano wadanda ake zargin
- Babban wanda ake zargi a kan kisan, Abatcha Bukar mai shekaru 23 ya amsa laifinsa cewa shine ya halaka marigayiyar
Jihar Borno - Jami'an rundunar yan sandan jihar Borno sun kama mutum shida da ake zargin suna da hannu a kan kisan Fatima Bukar, diyar Hon Bukar Abatcha, dan majalisa mai wakiltan mazabar Ngala a majalisar dokokin jihar Borno.
A makon jiya ne wasu suka shiga har gida suka kashe marigayiyar a yankin Gidan Dame da ke garin Maiduguri, babban birnin jihar.
Janar Alkali: Yadda Shari'ar Kisan Gillar Sojan Ke Wakana a Halin Yanzu, An Gabatar da Wadanda Ake Zargi
Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan sanda sun kama mijin marigayiyar bayan kisan sannan daga bisani suka sake shi kafin aka kama wadanda ake zargin sun aikata ta'asar da taimakon wayar marigayiyar.
Yadda aka kama mutum 6 kan kisan yar dan majalisar Borno
A cikin wata sanarwa da ya gabatarwa manema labarai a Maiduguri, jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Sani Kamilu Shatambaya, ya ce an kama babban wanda ake zargi cikin mutum shidan mai suna Abatcha Bukar mai shekaru 23 na yankin Gidan Dambe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin yan sandan ya bayyana cewa Bukar ya karbi bakin kashe marigayiyar.
Sauran wadanda ake zargin sun hada da Nuhu Mohammed mai shekaru 27 na yankin Gwange; Ismail Mohammed Barka mai shekaru 23 na yankin Gwange; Ibrahim Mustapha mai shekaru 28; Usman Yusuf mai shekaru 25 da Mohammed Yunus mai shekaru 29.
Wayar marigayiyar ya tona asiri
ASP Shatambaya ya ce kayayyakin da aka samo daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayar Infinix Hot 30i da hotuna biyu na raunin da ke hannun Abatcha Bukar.
Sanarwar ta ce:
"Ana iya tuna cewa a ranar 17 ga watan Oktoban 2023, da misalin karfe 6:00 na yamma, rundunar ta samu rahoto na kisan kai daga reshen Gwange na wata matar aure Fatima Alhaji Bukar ta yankin Gidan Dambe, Maiduguri. Haka kuma, a kokarin tabbatar da gaskiya a binciken, rundunar ta yi amfani da yan sanda sirri don gano tushen lamarin.
“A ci gaba da binciken, an gano cewa wayar marigayiyar ta bace a wurin da abun ya faru, don haka aka takaita bincike kan gano lambar IMEI dinta. Kokarin yan sanda ya haifar da sakamako mai kyau wanda ya kai ga kama wadanda ake zargi; Ibrahim Mustapha, Usman Yusuf, Muhammed Yunus, Nuhu Mohammed da Ismaila Mohammed Barka, dukkansu maza ne a yankin Gwange na garin Maiduguri, wadanda ke da hannu wajen batan wayar marigayiyar infinix Hot30i.
"An kama babban wanda ake zargi Abatcha Bukar mai shekaru 23 na yankin Gidan Dambe kuma ya amsa cewa shine ya kashe marigayiyar."
Kisan Fatima Bukar: Zulum ya sa ayi bincike
A baya mun ji cewa an kama mijin diyar dan majalisar da aka kashe bayan umarnin da gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya bayar ga hukumomi da su mayar da gawarta zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri domin a yi bincike kan gawar.
Ƙafin umarnin gwamnan dai, iyalanta sun shirya jana'izar ta da karfe 2:00 na rana a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, a gida mai lamba 707 a birnin Maiduguri.
Asali: Legit.ng