Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Fara Biyan Limamai da Masu Unguwanni Alawus

Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Fara Biyan Limamai da Masu Unguwanni Alawus

  • Gwamnatin jihar Katsin na cigaba da nemo hanyoyin da za ta bi domin magance matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar
  • Gwamnatin za ta fara biyan limamai da masu unguwanni alawus-alawus a duk ƙarshen wata domin ƙarfafa musu gwiwa wajen yaƙar rashin tsaro
  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da kwamitin gudanarwa na rundunar tsaro ta KCSWC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Katsina - Gwamnatin Katsina ta sanar da shirin bayar da alawus-alawus na musamman ga limaman masallatan Juma'a da mataimakansu da masu kiran Sallah da masu unguwanni domin karfafa musu gwiwa wajen yaƙar rashin tsaro a jihar.

Gwamna Dikko Radda ya sanar da hakan ne bayan ƙaddamar da kwamitin gudanarwa na rundunar tsaro ta Katsina Community Watch Corps (KCSWC), rahoton PM News ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Hotunan Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Sun Cika Gidan Kwankwaso Maƙil Kan Abu 1

Gwamna Dikko zai ba da alawus ga limamai
Gwamnatin jihar Katsina za ta fara ba limamai alawus Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Yadda kwamitin zai gudanar da aikinsa

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula-Mohammed ya fitar, gwamna Radda ya ce kwamitin zai hada kai da sauran jami’an tsaro wajen zaƙulo ƴan bindiga a faɗin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren yaɗa labaran na gwamnan ya bayyana cewa mambobin kwamitin gudanarwa na kowace ƙaramar hukuma a jihar sun haɗa da shugaban ƙaramar hukuma, hakimi, DPO na ƴan sanda da wakilan hukumomin tsaro daban-daban.

A cikin sanarwar da Ibrahim Kaula ya fitar, Sauran mambobin kwamitin su ne ƴan kasuwa da wakilan ƙungiyoyin addini.

Gwamnan ya ce kwamitin zai sa ido tare da tantance ayyukan KCSWC a yankunansu tare da gabatar da rahoton wata-wata ga kwamishinan tsaro na cikin gida.

Gwamnatin Katsina ba za ta tattauna da miyagu ba

Gwamnan jihar Katsina ya yi nuni da cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da ƴan bindiga masu tayar da ƙayar baya ba a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Fara Binciken Sarakunan Gargajiya Masu Taimakawa Yan Bindiga a Jiharsa

Gwamnatin ta tabbatar da cewa za ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin ta kare al'ummar jihar daga barazanar masu tada ƙayar baya.

Gwamna Radda Ya Shirya Kawo Karshen Yan Bindiga

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Katsina, Malam Umaru Dikko Radda, ya bayyana cewa a shirye yake ɗomin ya sadaukar da rayuwarsa wajen kawo ƙarshen ƴan bindiga a jihar.

Gwamnan ya yi nuni da cewa gwamnatinsa za ta fi bayar da fifiko a wajen tsaro domin magance matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng