Igboho Ya Caccaki Gumi Saboda Kalamansa Na Kawo Rashin Zaman Lafiya a Kasa
- Sunday Igboho, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa ya yi gargadi ga Sheikh Ahmed Gumi inda ya ce ya kula da kalamansa
- Igboho ya ce wannan gwamnati ba irin ta Muhammadu Buhari ba ce da zai shiga lamuran tattaunawa da sakarkarun ‘yan bindiga
- Matashin ya bukaci kowa ya ba da tashi gudunmawa don tabbatar da zaman lafiya a kasar ba tare da bambanci ba
Jihar Oyo – Ana ci gaba da caccakar Sheikh Ahmed Gumi saboda kalamansa kan Nyesom Wike da kuma gwamnatin Bola Tinubu.
Gumi ya zargin gwamnatin Tinubu da fifita Kiristoci da kuma kiran shugaban da ya tube Wike a mukaminsa tare da nada Musulmi, Tribune ta tattaro.
Wane sako Igboho ya tura wa Gumi?
Mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya soki Gumi inda ya ce malamin ba zai samu damar jagorantar tattaunawa da ‘yan bindiga da barazana ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Igboho ya ce Tinubu ya yi amfani da kwarewa ne wurin nada ministocinsa ba tare da nuna wariya ba, Naija News ta tattaro.
Ya ce wannan ba irin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba ce da ya yi kutun-kutun wurin tattaunawa da sakarkarun ‘yan bindiga.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata 24 ga watan Oktoba a Ibadan da ke jihar Oyo, Igboho ya ce bai kamata Gumi ya yi amfani da kalamansa wurin tarwatsa Najeriya ba.
Wane kira Igboho ya yi wa ‘yan Najeriya?
Ya ce:
“Mu na sane da tarihin Gumi da kuma salonsa, kafin zuwan Tinubu, irinsu Gumi kamata ya yi su na amsa tambayoyi da ya shafi harkar tsaro kan zargin hannunsa a cikin rikicin ‘yan bindiga.
“Ba za mu zuba ido muga irinsu Gumi na amfani da damarsu na tarwatsa kasar Najeriya ba da kawo rudani a hudubobinsu.
“Ba mu na goyon bayan Gwamnatin Tarayya ba ne amma kuma mu na da rawar da za mu taka a gyaran kasa, don haka akwai bukatar hadin kai a kasa.”
Ya kara da cewa don ganin an samu zaman lafiya dole kowa ya kaucewa maganganu da za su kawo matsala a tsakanin ‘yan kasa.
Igboho ya bai wa makiyaya wa’adin barin yankinsu
Kun ji cewa, mai fafautukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya bai wa makiyaya wa’adin kwanaki bakwai su bace daga yankin Yarbawa.
Igboho ya yi wannan gargadin ne yayin da ake ci gaba da kashe-kashe a yankin tsakanin manoma da makiyaya.
Asali: Legit.ng