Tsohon Sanatan PDP Ya Fadi Yadda Gwamnatin Buhari Ta Jefa Naira a Matsala
- Ben Murray Bruce ya soki yadda tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafiyar da tattalin arziki a mulkinsa
- Tsohon ‘dan majalisar dattawan ya zargi gwamnatin da ta shude da bankin CBN da buga kudi ba tare da sanin ‘yan majalisa
- Duk karyewar da Naira ta ke yi a kasuwa, Sanata Murray Bruce ya na ganin ba laifin gwamnatin shugaba Bola Tinubu ba ne
Abuja - Ben Murray Bruce ya sake magana kan halin tattalin arzikin da kasa ta shiga, ganin irin yadda darajar Naira ta karye a yanzu.
Sanata Ben Murray Bruce ya tofa albarkacin bakinsa ne a dandalin Twitter, ya soki tsarin musayar danyen mai da aka shiga da Najeriya.
‘Dan siyasar yake cewa kyau ‘yan majalisar tarayya su fito da doka wanda za ta haramta irin wannan yarjejeniya da gwamnati ta burma.
CN ya buga kudi babu lissafi
Baya ga haka, Murray Bruce mai shekara 67 ya yi Allah-wadai da yadda bankin CBN ya rika buga kudi a gwamnatin Muhammadu Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Sanatan ya ke cewa idan Mai girma Bola Tinubu ya nemi ya binciki gwamnatin da ta shude, hakan zai jawo tashin-tashina.
Baya ga haka, attajirin ya ce babu dalilin buga kudi barkatai ba tare da sanin majalisa ba, a cewarsa wannan ne sanadiyyar karyewar Naira.
Jawabin Ben Murray Bruce
"Meyasa gwamnati za ta karbi kudin kwangilar danyen mai kafin lokaci? Ta ya za a biya albashi? Ina ga abubuwan more rayuwa?
Tun farko bai kamata ayi wannan ba. Amma tun da aikin gama ya gama, ka da a maida hankali a kan binciken gwamnatin baya.
Abin da ya kamata a maida hankali a kai shi ne ganin hakan ba ta sake maimaituwa.
Daga cikin abin da ya jawo Naira ta ke faduwa saboda wannan aikin ne. Idan aka rika buga kudi su na yawo, za a shiga matsalar tattali."
- Ben Murray Bruce
Bola Tinubu zai magance tashin Dala
Dazu nan aka ji labari ta bakin Mista Wale Edun cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta na kokarin hana Dala cigaba da tashin kullum-yaumin a kasuwa.
Wale Edun ya ce an bi ta hannun kamfanin NNPC kuma ana yin tsari domin a rage kashe kudi da facaka domin ganin kudin Najeriya ya farfado.
Asali: Legit.ng