Duba wayar miji na daya daga cikin abunda ke kawo mutuwar aure – Mansurah Isah
Tsohuwar fitacciyyar jarumar Kannywood, Mansura Isah tayi magana akan zamantakewar aure da kuma abunda yasa aurenta da mai gidanta, Sani Musa Danja yayi karko.
Kamar yadda hasashe suka nuna, auren fitattun jarumai musamman na Kannywood baya karko sai dai labarin ya sha bamban a kan Mansurah da Danja domin a yanzu sun shafe tsawon shekaru 11 tare a matsayin mata da miji.
A hira da wata mujalla tayi da jarumar, an tambaye ta kan sirrin da yasa suka shafe shekaru 11 da aure ba tare da sun rabu ba.
Sai jarumar tace: “Inkiyar da ake kiran mijina shine mai buhu buhun yan mata. Kasancewa matar Sani Danja ba abune mai sauki bako kadan. Wasu lokutan, na kan zama makauniya, kurma kuma bebiya domin ganin auren nan ya rayu.
“Shi jarumi ne, kuma baya ga haka yana da kyau da kudi. Wadannan sune abubuwan da mata da dama ke so a namiji. Mata da yawa suna rokon ya so su.
“Na gina kaina sosai kan hakuri domin na fahimci irin namijin da nake aure. Ina auran shahararre ne saboda nima shahararriya ce kuma wasu lokutan masoyanka za su yi martani mai cike da wauta.
KU KARANTA KUMA: Gidan aro: Almakura ya mika wa Sule makullen gidan gwamnatin Nasarawa
“Mu kuke tsamanni daga auran mutumin da addininsa ya yarda yayi mata hudu? Daya daga cikin babban tubalin da na gina aurenmu akai shine ban taba duba wayarsa ba a rayuwata.
“Kun san cewa, dabi’ar mata na duba wayoyin mazajensu na daya daga cikin manyan abubuwan da ke sa mutuwar aure. Idan mace ta duba wayan mijinta sannan tag a abunda bai kamata ta gani ba, zai dame ta sosai, kuma zai iya kai ga kawo karshen auren. Amma idan ka kauracewa wayan mijinka, da duk wani abunsa na sirri, za ku zauna lafiya a aurenku. Ina ganin irin haka ne suka sa aurenmu yayi karko.”
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng