“Sai Kace a Karkara”: Matashiya Yar Najeriya Ta Baje Kolin Boyayyun Wuri a Turai

“Sai Kace a Karkara”: Matashiya Yar Najeriya Ta Baje Kolin Boyayyun Wuri a Turai

  • Wata mata yar Najeriya ta dauki bidiyon yadda ta dunga farautar neman gida a Birtaniya kuma ya yadu
  • Ta gano cewa gano cewa gidan da ta ke sha'awa bai dace da ita ba don haka ta fadi iya gaskiyar abun da ke zuciyarta
  • Ta kuma bayyana cewa wasu yankunan kasar Birtaniya sam basu da tsafta kamar yadda ta yi tsammani ta kwantanta su da Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wani bidiyo mai tsuma zuciya na fafutukar wata yar Najeriya da ta je neman gida a Birtaniya ya dauka hankalin masu amfani da soshiyal midiya da dama.

Ta nadi bidiyon tafiyarta zuwa wajen duba wani gida da ta gani a soshiyal midiya, amma sai gwiwowinta suka sace da abun da ta gani a zahiri.

Matashiya tana magana
“Sai Kace a Karkara”: Matashiya Yar Najeriya Ta Baje Kolin Boyayyun Wuri a Turai Hoto: TikToK/@abebioge
Asali: TikTok

Ta kuma nuna banbanci tsakanin hadaddun hotuna na Birtaniya da ta gani a yanar gizo da kuma unguwanni masu datti da kazanta da ta ci karo da su a hanyarta ta zuwa ganin gidan.

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Ajiye Girman Kai, Ya Roki Budurwarsa Ta Hanyar Birgima a Kasa, Bidiyon Ya Bazu

Ta nuna rashin gamsuwarta da gidan, tana mai cewa ya yi nisa sosai daga tashar jirgin kasa mafi kusa kuma cewa ba za ta ji dadin tafiya ita kadai a cikin duhu ba bayan ta sauka daga jirgin kasan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon nata wani karin haske ne na zahirin gaskiya da ban dariya game da kalubalen da ke tattare da samun gidan haya da ya dace a wata kasa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

LaDotsPartycity ta yi martani:

"Na ga wuraren da suka fi wannan muni a UK lokacin hutu. Abu mai kyau ne da kika ki karbar gidan. Tsaro da lafiyanki na da muhimmanci. Masha Allah."

Sammy Grant:

"Nan UK ne ko dai wani wuri a Najeriya."

Adeeyitayo ta rubuta:

"Wajen farkon ya yi kama da kauyen Agbomonrin fa."

Damiloxwine ta yi martani:

Kara karanta wannan

"Ga Kyau, Ga Kuruciya”: Dan Najeriya Ya Tarbi Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya a Filin Jirgin Sama, Bidiyo

"Yankin UK da ba za su nuna mana ba."

Alertcomedy:

"Wannan wurin ya yi kama da malete."

Bisola:

"Me yasa yan Igbo basa daura murya a bidiyo baaba ina son Yarbawa da yawa."

Bidiyon wani ango da amaryarsa ya girgiza intanet, an hango masu matsala

A wani labarin, mun ji cewa wani bidiyon amarya da ango suna kiciniyar fita daga kofa a lokaci guda ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Shafin @axmedzaki440 ne ya wallafa bidiyon mai rikitarwa a dandalin TikTok kuma ya samu kimanin mutum miliyan 14.5 da suka kalla a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng