Nyesom Wike Ya Farfado da Doka, Marasa Biyan Haraji Za Su Tafi Kurkuku a Abuja
- Ezenwo Nyesom Wike ya na so a tabbatar da dokar biyan haraji ta na aiki a birnin Abuja domin asamu kudin shiga masu yawa
- Ministan ya fitar da sanarwa cewa ma’aikatu da hukumomin banki da bankuna su rika tambayar takardar shaiar TCC ta biyan haraji
- Duk wani wanda aka samu ya saba doka, Wike ya yi na’am da hukunta shi, hakan zai iya zama cin tarar kudi ko zaman gidan yari
Abuja - Ministan birnin tarayya watau Abuja, Ezenwo Nyesom Wike zai sake shigowa labarai kwanaki bayan an fara kiran a tsige shi.
Wannan karo, Daily Trust ta ce Barista Ezenwo Nyesom Wike ya nemi a dabbaka tsarin karbar haraji kamar yadda ya zo dokar Abuja.
Sabon Ministan ya dauki mataki ne saboda a samu kudin shiga domin yin ayyuka.
Nyesom Wike zai tara kudi a Abuja
Kwanakin baya aka ji gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Bola Tinubu, ta ba FCTA damar fita daga cikin asusun TSA na bai-daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanadiyyar umarnin da ministan ya bada, duk wata ma’aikata, cibiya ko hukumar gwamnati ko banki za su dage wajen tattaro haraji.
Abuja: Dokokin haraji za su yi aiki
Umarnin ya zaburar da duka ma’aikatu da kuma bankunan kasuwa su dage musamman wajen tabbatar da sashe na 85 na dokar PITA.
Business Day ta ce umarnin ministan zai tabbatar da aikin sashe na 31 na dokar harajin birnin tarayya wanda aka fito da ita a shekarar 2015.
Dokokin sun bukaci hukuma ko banki ya nemi ganin takardar shaidar biyan haraji na TCC kafin a iya yin wani ciniki a fadin birnin na Abuja.
Ina hukuncin kin biyan haraji a Abuja?
Hukuncin wanda aka samu ya sabawa wannan doka ya fara ne daga tarar N100, 000.
Baya ga biyan tara, idan har laifin ya yi yawa, kotu za ta iya yankewa mutum daurin shekaru uku a gidan gyaran hali idan har ya saba doka.
Wani babban jami’in da ke kula da tsare-tsaren tattali da samun haraji, Chinedum Elechi ya shaidawa ‘yan jarida wannan a ranar Litinin.
Ana kukan tsadar rayuwa a yau
Mafi yawan al'ummar Najeriya su na faman kokawa a game da 'dan karen tsadar rayuwa kamar yadda aka samu labari a wani rahoto dazu.
Cire tallafin da aka yi ya jawo farashin man fetur ya karu da kusan N500 sannan kudin gas da ake saye domin yin girki ya tashi a yanzu.
Asali: Legit.ng