Watakila a Shawo Kan Tashin Dala, Ana Sa Ran Shigowar $10bn Kwanan Nan Inji Edun
- Ministan tattalin arzikin Najeriya ya halarci taron NES a birnin tarayya na Abuja, ya yi magana a kan tsarin da ake da shi
- Ganin yadda Naira ta ke cigaba da karyewa, Wale Edun ya ce sun nemo $10bn daga waje domin a farfado da darajar kudin kasar
- Dalar Amurka ta dade da haura N1000 a kasuwar canji, Edun ya shaida cewa ana fama da karancin kudin ketare a bankuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - A wajen wani taro da NES ta shirya a garin Abuja, Ministan tattalin arziki, Wale Edun ya yi magana game da halin da ake ciki a yau.
A ranar Litinin The Cable ta rahoto Mista Wale Edun ya na cewa nan da ‘yan makonni kadan ake sa ran samun $10bn na kudin kasar waje.
Ministan tattalin arzikin ya shaidawa Najeriya cewa sun san inda su ka dosa, kuma cikin makonni kudin za su iso ba sai an dauki watanni ba.
Matakan da za a dauka domin Naira ta mike
A jawabin da ya gabatar, ministan ya nuna za a rage kashe kudi kuma za a nemi masu hannun jari saboda a samu darajar Naira ta farfado.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Baya ga samun kudin ketare ta hannun NNPC, kara yawan samar da kayayyaki, rage kashe kudi, ciniki, daga tattaunawarmu da asusun SWF, sun shirya fara ba m kudi tare da zuba hannun jari, akwai maganar $10bn na kudin kasar waje da za a samu a cikin makonni masu zuwa ba watanni ba."
- Wale Edun
Tattalin arziki: Yunkurin Bola Tinubu
Edun ya tabbatarwa majalisar NES da cewa gwamnati ta kama hanyar inganta tattalin arziki.
Business Day ta rahoto shi ya na mai cewa a ranar Alhamis Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu a wasu kudiori biyu da za su jawo Dala ta sauka.
Wadannan kudirori da sun zama cikakkun dokokin kasa za su bada dama kudin da aka dankare a wurare dabam-dabam su dawo cikin bankuna.
Yayin da Dala ke ta tashi, Ministan ya koka da cewa akwai karancin kudi a bankuna.
Sabon tsarin Babban Bankin Najeriya
Ana da labari CBN zai cigaba da bada kudi domin shigo da abinci da wasu kayayyaki 43, watakila idan kaya su ka yi yawa, farashin abinci zai ragu.
Wani masanin tattalin arziki a jami’ar ABU Zariya, Dr. Usman Bello ya fada mana abinci ba zai sauka ba idan dai Dala ta na tsada a kasuwar canji.
Asali: Legit.ng