Ba a Gama Fama da ’Yan Bindiga ba, ‘Yan Ta’adda Sun Bulla a Jihar Kaduna
- A wani kauye da ake kira Kuyello a karamar hukumar Birnin Gwari, mutane su na rayuwa cikin fargabar zama da ‘yan ta’adda
- ‘Yan kungiyar Ansaru sun nemi wurin zama a yankin da aka dade ana fama da rashin tsaro, amma mutane ba su ba su mafaka ba
- A lokacin da ake fama da ta’adin ‘yan bindiga, ‘yan ta’addan su na neman yadda za su kara yawan mabiya a garin na Birnin Gwari
Kaduna - Mutanen kauyen Kuyello a karamar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna, sun koka game da bayyanar ‘yan ta’addan Ansaru.
Mazauna yankin na Birnin Gwari sun ce ‘yan kungiyar nan ta Ansaru sun ziyarce su, Daily Trust ta ce abin ya tada hankalin al’umma sosai.
Kwatsam sojojin kungiyar su ka shigo Kuyello, duk da ba su zo da fitina ba, mazauna kauyen sun nuna ba su gamsu da zama a cikinsu ba.
Ba a karbi 'Yan Ansaru a Birnin Gwari ba
Masu zama a kauyen su na tsoron ‘yan ta’addan su dauki matasansu, su cusa su cikin tafiyarsu, hakan zai kara masu karfi a Birnin Gwari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganin hakan aka turawa ‘Yan Ansaru malamai da su ka fada masu ba a sha’war shigowarsu, ‘yan ta’addan ba su ji dadin wannan magana ba.
Rahoton ya ce dakarun kungiyar ta’addancin sun fusata da martanin malamai, su ka sanar da al’ummar Kuyello za su shigo da karfi da yaji.
Ansaru su na auren 'yan matan Birnin Gwari
Wani shugaban al’umma a kauyen, Muhammadu Kuyello ya ce sun ga Ansaru sun shigo layin Dan Auta ba tare da yi wa koma magana ba.
A cewar Malam Muhammadu Kuyello, wadannan mutane sun fi zama a cikin jeji, sai yanzu ne su ke neman yadda za su tare a garin na su.
Da Dumi-dumi: Harin Fashi a Bankuna: Jami’an Tsaro Sun Cafke Mutane 4 a Jihar Arewa, Sun Fadi Yadda Aka Yi
Abin ya kai ‘yan ta’addan sun auri wasu daga cikin matan da ke wannan babban gari.
"Akwai Ansaru a gabashin Birnin Gwari"
Legit.ng Hausa ta tuntubi wani magidanci mazaunin Birnin Gwari wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar mana da wannan labari.
"Lallai ‘Yan Ansaru su na nan a gabashin Birnin gwari, kuma su na ta fadada ayyukansu na kiran al’umma, sun fi yawa a garin Damari.
Tun tuni su ke jawo mutane domin ganin mabiyansu sun karu, ta kai kwanakin baya sun yi artabu da fulanin daji, yanzu su na neman mafaka."
- Inji wanda aka yi hira da shi
Danyen aikin Israila a zirin Gaza
Ganin daruruwan mutane da aka kashe a Gaza, kwanakin baya aka samu rahoto cewa Fafaroma da Majalisar dinkin duniya sun soki Israila.
Kafin nan, sojojin Israila sun hallaka mutane a wani sansani da ke Arewacin yankin Jabalia, hakan ya jawo kasashen musulmai su ka kira taro.
Asali: Legit.ng