Bishiya Ta Yi Ajalin Mutane 2 a Jihar Kwara Bayan Ta Fado Kan Ma Su Jiran Abin Hawa

Bishiya Ta Yi Ajalin Mutane 2 a Jihar Kwara Bayan Ta Fado Kan Ma Su Jiran Abin Hawa

  • Mutane biyu sun rasa rayukansu bayan wata katuwar bishiya ta fado a kansu yayin da su ke jiran motar kasuwa a jihar Kwara
  • Lamarin ya faru ne a yau Litinin 23 ga watan Oktoba a Ilorin babban birnin jihar Kwara wanda ya ta da hankulan jama’a
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Okasanmi Ajayi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mutane biyu sun mutu

Jihar Kwara – Wata bishiya ta yi ajalin wasu mutane biyu yayin da wasu mutum 10 su ka ji raunuka a jihar Kwara.

Iftila’in ya faru ne a yau Litinin 23 ga watan Oktoba a Ilorin babban birnin jihar Kwara wanda ya ta da hankulan jama’a, cewar Tribune.

Mutane biyu sun mutu yayin da bishiya ta fado kan jama'a
Bishiya Ta Yi Ajallin Mutane 2 a Jihar Kwara. Hoto: Facebook.
Asali: Twitter

Meye ya jawo mutuwar mutanen a Kwara?

Wadanda abin ya rutsa da su na jiran mota a gefen hanya kusa da gidan man Baystar a Zango-Kulende da ke birnin Ilorin.

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Rasa Ranta Bayan 'Yan Ta'adda Sun Yi Mata Yankan Rago a Jihar Arewa, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faduwar bishiyar ya faru ne da misalin karfe 8 na safe wanda ya kawo rudani bayan yin ajalin wasu biyu nan take.

Har ila yau, faduwar bishiyar ya haddasa wayoyin wutar lantarki faduwa kan shaguna da lalata musu dukiyoyi.

Wane martani ‘yan sanda su ka yi a Kwara?

Mutane 10 da su ka sa mu raunuka an kwashe su zuwa asibiti mai zaman kansa na Olutayo da ke bayan gidan mai din da abin ya faru.

Wasu daga ciki an sallame su bayan ba su kulawa yayin da wadanda raunukansu su ka munana aka mika su zuwa babban asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Okasanmi Ajayi ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin 23 ga watan Oktoba, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Zaben Gamnan Kogi: Tashin Hankali Yayin da Magoya Bayan APC Da SDP Suka Yi Musayar Wuta

Har ila yau, kwamishinar lafiya a jihar, Amina El-Imam ta tabbatar da cewa mutum daya ya mutu dalilin faruwar faduwar bishiyar.

‘Yan sanda sun kama mutane 4 kan zargin fashin bankuna

A wani labarin, jami’an tsaro sun kama wasu mutane hudu da ake zargin sun kai farmaki a bankuna a jihar Benue.

Yayin harin, ‘yan fashin sun yi ajalin DPO da wasu jami’an ‘yan sanda guda uku a Otukopo da ke jihar

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.