Gwamnatin Jihar Borno Ta Haramta Barace-Barace da Zaman Banza
- Gwamnatin jihar Borno ta haramta barace-barace da zaman banza a wasu yankunan jihar da ke Arewacin Najeriya
- Rahoto ya bayyana wuraren da gwamnati ta hana wadannan dabi'u masu kawo koma-baya ga al'umma
- Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fuskantar barace-barace da ke kaiwa ga ayyukan ta'addanci
Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta haramta barace-barace a kan tituna a ciki da wajen birnin Maiduguri da karamar hukumar Jere, rahoton Leadership.
Haramcin na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida, Farfesa Usman Tar ya fitar a ranar Lahadi a Maiduguri.
Sako daga gwamantin Borno
Sanarwar ta kuma bayyana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Barace-barace a kan tituna da zaman banza ba sa daga cikin halinmu a Borno. Mu mutane ne masu daraja.
“Muna sanar da jama’a cewa gwamnatin jihar Borno ta sanya dokar hana fita a duk wani nau'in barace-barace da zaman banza a tsakanin garin Maiduguri da kewaye da karamar hukumar Jere.
“Haramcin ya shafi wurare kamar haka: Dukkan gine-ginen gwamnati, duk wasu wuraren ibada, duk wasu cibiyoyin kasuwanci, Sakatariyar Musa Usman, Kasuwar Monday, Tsohuwar Kasuwar Maiduguri, Kasuwar Budum, Titin Legas, Unguwar Kwastam, yankin Ofishin Wasiku, Mahadar Galadima , Mahadar Kwamishinan ‘yan sanda, titin Damboa, titin Baga, titin Dandal da sauransu.”
Yaushe dokar za ta fara aiki?
A cewar sanarwar, haramcin ya fara ne da nan take kuma za a dauki mataki kan wadanda suka ketare umarnin gwamnatin jihar, Within Nigeria ta tattaro.
Ba jihar Borno kadai ke fuskantar barace-barace ba, kusan dukkan jihohin Najeriya ne ke cikin wannan hali, to amma meye tanadin gwamnati na yaki da zaman banza?
An farmaki gwamnan jihar Kogi
A wani labarin, gwamnatin jihar Kogi a ranar Lahadi ta ce jami’an tsaro sun dakile wani yunkurin kisa da aka yiwa gwamnan jihar Yahaya Bello, The Nation ta ruwaito.
A cewar gwamnatin, an farmaki gwamnan ne a jiharsa da ke da tazarar kilomita kadan da babban birnin tarayya Abuja, a kan hanyarsa ta zuwa wani aiki daga birnin Lokoja.
Sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya fitar a Abuja, ya ce an kai harin ne da misalin karfe 4 na yamma. a ranar Lahadi, 22 ga Oktoba, 2023.
Asali: Legit.ng