Sojojin Isra’ila Sun Harba Sabon Roka a Gaza, Sun Yiwa Mutum 55 Kisan Gilla
- Rahoto ya bayyana yadda sojojin Isra'ila suka yiwa mazauna Zirin Gaza kisan gilla a cikin wannan makon
- An bayyana mutuwar akalla mutane 55 a harin da aka kai a ranar Lahadi, lamarin da ya dauki hankali
- Ana ta kai farmaki kan al'ummar Falasdinu tun bayan da Hamas ta kai hari kan mutanen Isra'ila
Gaza, Falasdinu - Wani kazamin farmakin cikin dare da sojin Isra'ila suka kai kan mutanen da basu ji ba basu gani ba a Zirin Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 55 a daren Lahadi.
A cewar hukumomin kasar, mutum 55 ne suka yi shahada a harin da sojin na Isra'ila ke ci gaba da kaiwa Falasdinawa tun rikicin da ya barke a ranar 7 ga watan Oktoba.
Hukumomin sun kuma bayyana cewa, Isra'ila ta rushe gidaje sama da 30 a cikin kankanin lokaci a farmakin da ya dauki sa'o'i kadan, Channels Tv ta ruwaito.
An kashe mutum 4,300 a Gaza
Gwamnatin Hamas ta kuma bayyana cewa, fiye da mutane 4,300 wadanda galibinsu fararen hula ne Isra'ila ta kashe yayin da Hamas ta kashe Isra'ilawa sama da 1,400, The Telegraph ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A tun farko, Isra'ila ta girke daruruwan dakarunta a Zirin Gaza don daukar fansar farmakin da Hamas suka kai kan Isra'ila a makwanni biyu da suka gabata.
A baya, kakakin rundunar sojin Isra'ila ya shaidawa duniya cewa:
"Daga yau, za mu kara adadin kai farmaki da takaita hadari. Za mu kara adadin farmaki kuma ina kira ga mazauna Birnin Gaza da su koma kudanci don tsira da lafiyarsu."
Akalla mutane sama da milian 1.1 ne a Arewacin Gaza da Isra'ila ke turawa gargadin barin yankin zuwa Kudanci.
Isra'ila na barazanar karar da Falasdinawa
Ministan Makamashi a Isra’ila, Israel Katz ya sha alwashin dakile taimakon da su ke kai wa Gaza idan ba a sake musu ‘yan uwa ba.
Katz ya bayyana haka ne a yau Alhamis inda ya ce duk wata hanyar taimako za su datse ta wanda su ke taimakon Gaza da su, cewar AlJazeera.
A ranar Asabar ce 7 ga watan Oktoba, kungiyar Hamas ta kai wani mummunan hari Isra’ila wanda ya yi ajalin mutane da dama, cewar Channels TV.
Asali: Legit.ng