Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Sheke Wani Kasurgumin Shugaban Yan Bindiga a Bauchi
- Sojoji sun yi nasarar kai wani kasurgumin dan bindiga kasa bayan da ya aikata mummunan barna a jihar Bauchi
- An bayyana yadda aka farmaki tawagar kasurgumin dan bindigan da ya addabi wani yankin Ningi
- Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fuskantar barnar tsagerun 'yan bindiga, musamman a wannan shekarun
JIhar Bauchi - Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka wani kasurgumin shugaban 'yan bindigan da gungun yaransa suka addabi al'umma a karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi, The Nation ta ruwaito.
Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an hallaka dan ta'addan mai suna Ya'u ne a wani farmakin da sojojin suka kai maboyarsa a wani yanki da ake kira Burra a Ningi ranar Juma'a.
An kuma ruwaito cewa, Ya'u da yaransa sun addabi yankin na Burra da munanan hare-hare ta hanyar amfani da miyagun makamai tare da sace mutane da neman kudin fansa.
Yadda lamarin ya faru
Majiyar kauye a Burra ta bayyana cewa, an sheke dan ta'addan ne a ranar Alhamis a yayin da dan ta'addan ke kan hanyar komawa maboyarsa a yankin bayan aikata barna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutuwar wannan kasurgumin dan ta'adda dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kakakin rundunar sojin Najeriya, Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, rahoton Daily Post.
A cewar sanarwar, jami'an soji sun yi amfani da bayanan sirri ne wajen gano motsin 'yan ta'addan da suka addabi jihohin Arewa.
Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fama da barnar 'yan bindiga masu sace mutane tare da karbar kudin fansa ba gaira babu dalili.
An kokarin kawo hanyar magance tsaro
A wani labarin, mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, zai jagoranci tawagar manyan jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya zuwa babbar taron kungiyar shugabannin ‘yan sanda na kasa da kasa na 2023 a San Diego, Carlifornia, Amurka.
Taron, mai taken 'The Real Advantage', an shirya shi ne don samar da dandali mai kima ga shugabannin 'yan sanda da kwararrun jami'ai a duk fadin duniya don aiki tare wajen tabbatar doka da oda a duniya.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Lahadi, tuni an fara taron tsakanin ranar 14 zuwa 17 ga watan Oktoba, 2023.
Asali: Legit.ng