Shugaban Hukumar EFCC Ya Shiga Ofis, Zai Iya Bankado Binciken Tsofaffin Gwamnoni

Shugaban Hukumar EFCC Ya Shiga Ofis, Zai Iya Bankado Binciken Tsofaffin Gwamnoni

  • Ola Olukoyede ya dare kujerar da Abdulrasheed Bawa ya bari a EFCC, zai fara binciken wadanda ake zargi da taba dukiyar kasa
  • Kafin zuwansa, Hukumar EFCC ta na binciken wasu manyan ‘yan siyasa da sun rike mukamai a jihohinsu, FEC da majalisar tarayya
  • Gwamnati ta dade ta na shari’a da wasu da su ka rike mukamai shekaru da-dama da su ka wuce, har an manta da zamaninsu a yau

Abuja - Ola Olukoyede ya shiga ofis a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.

A ranar Lahadi, Punch ta ce Ola Olukoyede ya gaji binciken da ake yi a kan wasu tsofaffin Gwamnoni, Ministoci da Sanatoci a hukumar EFCC.

Mista Ola Olukoyede ya na da babban aiki a gaban shi bayan ya canji Abdulrasheed Bawa. Ana zargin N772.2bn da $2.2bn sun yi kafa a kasar.

Kara karanta wannan

Shetty, El-Rufai da Sauran Mutum 5 da Tinubu Ya Ba Mukamai, Sai Ya Dawo Ya Karbe

EFCC na binciken Tsofaffin Gwamnoni
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede Hoto: officialEFCC
Asali: Twitter

Ana binciken tsofaffin Gwamnoni a EFCC

Daga cikin tsofaffin Gwamnonin da EFCC ta gayyata domin ayi bincike a kan su akwai Dr Dr. Kayode Fayemi, Ayo Fayose da Bello Matawalle.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyin EFCC ba su hakura da binciken tsohon Gwamnan Enugu, Sanata Chimoroke Nnamani ba duk da kotu tarayya ta wanke shi a shekarar 2018.

A 2010 aka zargi Sanata Abdullahi Adamu da satar dukiyar jihar Nasarawa. Wani Gwamna a jerin nan shi ne Peter Odili da ya yi mulki a Ribas.

EFCC ta taba yi wa Rabiu Kwankwaso tambayoyi a game da inda N10bn su ka shige a asusun kudin fansho yayin da ya ke Gwamnan Jihar Kano.

Rahoton ya ce EFCC ta na binciken tsohon Gwamnan Abia, Theodore Orji da ‘ya ‘yansa kamar yadda aka taba shari’a da Alhaji Sule Lamido.

An fara manta inda EFCC ta kwana

Kara karanta wannan

Badakalar Kwangila: Shugaban EFCC Ya Tona Asiri Kan Asarar da Najeria Ta Yi Cikin Shekaru 3 Na Buhari

Akwai zargin karkatar da N5bn a kan Danjuma Goje, daga baya aka shiriritar da binciken.

Sauran tsofaffin Gwamnoni da ke da takarda a EFCC su ne: Aliyu Wammako (N15bn), Timipre Sylva (N19bn) da Sylva Sullivan Chime (N23bn)

Ragowar su ne Murtala Nyako, Ali Modu Sheriff, Babangida Aliyu, Jonah Jang, Lucky Igbinedion, Ikedi Ohakim da kuma irinsu Gabriel Suswam.

Mutanen Goodluck Jonathan

Akwai binciken Kanal Sambo Dasuki da Diezani Alison-Madueke da ya ki zuwa karshe, sun rike mukami ne a lokacin Goodluck Jonathan.

Haka zalika akwai Sanata Stella Oduah da ta taba zama Ministan harkokin jiragen sama.

Nadin shugaban EFCC ya saba doka?

Sakataren kungiyar CEDEHUR ya ce zaman lauya shugaban EFCC zai ci karo da dokar EFCC, kamar yadda aka ji, tuni aka yi masa raddi.

A cewar Adebayo Ogorry, hukumar EFCC ba ta fararen hula ba ce, dole shugabanta ya zama babban jami'in ‘Dan Sanda da ya dade ya na aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng